Ni ne wanda IBB yake burin ya zama Shugaban kasa inji Tsohon Hadimin Jonathan, Obasanjo
- Doyin Okupe ya na ganin shi ya fi kowa cancanta ya rike Najeriya a 2023
- Okupe yace ya cika sharudan da IBB ya bada na wanda ya dace da mulki
- ‘Dan siyasar yace ya san jama’a a ko ina, kuma yana cikin ‘yan shekara 60
Abuja - Tsohon hadimin shugaban kasa, Dr. Doyin Okupe ya ce shi ne ya fi dace wa da ya dare a kan kujerar shugaban Najeriya a zabe mai zuwa.
Meyasa Doyin Okupe ya fi kowa cancanta?
Doyin Okupe yake cewa shi tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida Babangida yake da shi a rai da yake maganar wanda ya dace da mulki.
Da aka yi hira da shi a Arise TV dazu, Doyin Okupe yace babu shakka Ibrahim Badamasi Babangida shi ya hango da yake batun siyasar 2023.
“Na yarda da shi da ya dace ya kamata shugaban kasan ya zama ‘dan shekara 60, misali idan ni na shiga takara, ina shekara 60.”
“Ina tunani da Janar Babangida yake magana, duk da ban zauna da shi ba, amma jikina ya na fada mani, ni yake tunani a ransa.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Da gaske na ke yi, domin babu karamar hukumar da ban shiga akalla sau biyar a kasar nan ba, babu, kuma na shirya rike kasar nan."
Daily Trust ta rahoto Okupe ya na cewa bayan aiki da ya yi da Goodluck Jonathan da Olusegun Obasanjo, aboki yake gare su, kuma ya ga yadda ake mulki.
Daga ni sai Osinbajo idan ana batun 2023 - Okupe
Doyin Okupe wanda ya yi aiki da tsofaffin shugabannin kasa biyu a baya, ya ce shi da Farfesa Yemi Osinbajo ne suka cika ka’idojin da Janar Babangida ya sa.
“Idan ka yi la’akari da kyau, ni Doyin Okupe ya kamata a fara magana. Daga nan sai kuma Osinbajo, idan aka dauki ka’idojin da na auna kai na da su."
Okupe yake cewa Osinbajo bai iya amfani da damarsa na mataimakin shugaban kasa ba saboda siyasar APC, amma ya ce mutum ne mai ilmi da basira sosai.
Da aka yi hira da shi kwanaki, tsohon shugaban kasar na mulkin soja, Babangida ya yi waje da irinsu Atiku Abubakar da Bola Tinubu daga cikin takarar 2023.
Janar Babangida mai ritaya ya ce ya kamata a samu wani 'dan shekara 60, wanda ya lakanci ilmin tattalin arziki, kuma ya ke da abokai a ko ina a kasar nan.
Asali: Legit.ng