Iyalaina da Abokaina Sun Matsamun Na Nemi Shugabancin Kasa a 2023, Gwamna

Iyalaina da Abokaina Sun Matsamun Na Nemi Shugabancin Kasa a 2023, Gwamna

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya bayyana cewa yana shan matsin lamba daga iyalai da abokanan arziki
  • Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da ya karbi bakuncin wasu ƙungiyoyi dake neman ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023
  • Muhammed, wanda ya nemi a bashi mako 3 ya yi shawara, ya sake neman a sake ba shi lokaci

Bauchi - Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi, yace iyalansa da abokanan arziki sun matsa mai lamba ya nemi takarar shugabancin kasa a zaɓen 2023 dake tafe, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da ya karbi bakuncin kungiyar matasan arewa da kungiyar direbobi (NURTW) da wasu kungiyoyi a gidan gwamnati dake Bauchi, ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Ni fa sulhu kawai naje yi: Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa kan zaman sukar Buhari

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed
Iyalaina da Abokaina Sun Matsamun Na Nemi Shugabancin Kasa a 2023, Gwamna Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Meyasa bai amsa kiran mutane ba?

Da farko gwamnan ya nemi masu kiraye-kiraye da kunguyoyi su bashi mako uku yayi nazari tare da tuntubar wasu mutane kan ya fito takarar ko kada ya fito.

Sai dai bayan makwanni ukun da ya nema sun shude, gwamna Muhammed ya sake neman a bashi wasu mako ukun domin yanke hukunci na karshe.

A halin yanzun, Gwamnan jihar Bauchi ya sake neman karin lokaci domin yanke hukunci, ranar Alhamis.

Abokaina da iyalaina sun matsamun

A jawabinsa, Gwamna Bala Muhammed, yace:

"Tun a baya abokanaina sun matsamun lamba na nemi takara, iyalaina suka nuna goyon bayansu. Jam'iyyar PDP reshen jihar Bauchi ta roke ni na nemi takarar nan."
"Har yanzun muna cigaban da yin shawara ne. A baya da kuka zo na faɗa muku akwai bukatar in yi shawara."

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ne matashin dan takarar da zai iya gyara Najeriya, in ji wani sanatan Kogi

"Hakazalika a yanzun ma zan nemi alfarmar ku bani wani lokaci, akwai bukatar nazari sosai kan lamarin ne shiyasa muke cin lokaci. Ina mai baku hakuri."

Muhammed ya gode wa haɗakar kungiyoyin baki ɗaya bisa ganin cancantarsa da suka yi kuma suka nemi ya fito takara, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Ya kara da cewa wannan ba shine karo na farko da aka bukace shi da ya fito takarar shugaban ƙasar Najeriya ba.

A wani labarin kuma Fitacciyar Jarumar a Masana'antar Shirya Fina-Finai, Simela, Ta Rigamu Gidan Gaskiya

Jarumar, wadda tana shirya fina-finai sannan tana bada umarni ta mutu ne sanadiyyar haihuwa a gadon asibiti, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Makusantan jarumar mai shekara 38 a duniya sun kai ta asibiti ne domin kula da lafiyarta bayan ta samu matsala lokacin haihuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel