APC da PDP duk jirgi daya ne: Jega ya gargadi 'yan Najeriya cewa su guje masu

APC da PDP duk jirgi daya ne: Jega ya gargadi 'yan Najeriya cewa su guje masu

  • Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ya caccaki jam'iyyun APC da PDP
  • Ya shaida wa 'yan Najeriya cewa, dukkaninsu daya suke, kuma basu tsinana komai ga kasa ba
  • Ya bayyana cewa, a tsawon aikinsa, ya ga abubuwan ban tsoro dangane da tsarin mulkinsu

Tshon shugaban hukumar INEC, farfesa Attahiru jega ya gargadi 'yan Najeriya kan sake zaban shugabanni daga jam'iyyun APC da PDP.

A cewarsa, wadannan jam'iyya dukkansu hali daya suke tafe akai, kuma babu abinda suka taba wa 'yan Najeriya tsawon shekaru 20 da suka yi suna mulki.

Jega ya bayyana haka ne yayin wata hira da sashin Hausa na BBC, wanda Legit Hausa ta tattaro yana cewa, babu bukatar sake yin imani da jam'iyyun a nan gaba kasancewar sun gagara cimma wani abin kirki tsawon shekaru.

APC da PDP duk jirgi daya ne: Jega ya gargadi 'yan Najeriya cewa su guje masu
Farfesa Attahiru Jega | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewar Jega:

"APC da PDP sun yi [mulki] duk mun gani, ba gyara suke nufi ba.

Kara karanta wannan

An gina APC kan karairayi, bacin sunan jama'a, ba za ta wuce 2023, Lamido

"Idan ka dubi yaki da cin hanci da rashawar nan, duk mutanen da ake cewa barayi ne za a hukunta su saboda sun yi sata a karkashin PDP, yanzu sun lallaba sun koma APC, kuma shiru kake ji, don haka ne ni tuni na yi rijista da PRP na zama dan jam'iyya don duba ta yadda zan taimaka wa Najeriya'.
"Shi ya sa mu muke ganin cewa yanzu lokaci ya yi da za a samar da wata dirka da duk mutumin kirki zai koma cikinta, domin bayar da tasa gudunmawar wajen kawo gyara a Najeriya''.

Bai kamata a bar mabarnata suna mulkin kasar nan ba

A bangare guda, Jega ya kuma bayyana bukatar mutanen kirki da su shigo a dama dasu a siyasa, domin bai kamata a bar mabarnata su ci gaba da cin karensu babu babbaka ba, a cewarsa.

Da yake koka kan yadda 'yan siyasa ke mulki yadda suka ga dama, malamin na jami'a ya bayyana karara cewa, tsawon shekaru 40 na aikinsa ya gane cewa:

Kara karanta wannan

Hushpuppi: DCP Abba Kyari na fuskantar barazanar kora daga aiki da gurfanarwa, Hukumar ‘yan sanda

"A gaskiya yadda na ga 'yan siyasarmu na tafiyar da lamarin zabe da kuma yadda suke wakilci idan an zabe su, to gaskiya akwai abun tsoro."

Tsohon shugaban na INEC ya kara da cewa rashin shugabanci na gari ne ya haifar da dukkan matsalolin da Najeriya ke fama da su, har ta kai ga wasu na neman a raba kasar a halin da ake ciki.

Dattijon Arewa ya caccaki mulkin APC, ya ce za ta ruguza Najeriya kafin 2023

Kakakin kungiyar dattawan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya caccaki jam’iyyar APC, kan yadda take tafiyar da Najeriya, yana mai cewa nan da shekarar 2023, jam’iyyar da ke mulki za ta ruguza al’ummar da ta fi yawan jama’a a Afirka.

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da yayi da gidan Talabijin na Channels na Politics Today a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli.

A cewarsa, jam'iyyar siyasa ta gaba da za ta karbi ragamar shugabanci a 2023 za ta gamu da aiki na gyara kasar.

Kara karanta wannan

Dabbobi Sun Fi Su Gata, Baƙar Wuya Suke Sha a Hannun DSS: Lauya Ya Faɗa Halin Da Muƙarraban Igboho Ke Ciki

Wata kungiya ta yi kira da a mika Najeriya ga gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed

A wani labarin, kungiyar matasan Arewa a karkashin inuwar kungiyar Concerned Citizens Like-Minds (CCLM) ta ce Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi shi ne mafi cancanta wajen tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, jaridar Sun ta ruwaito.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya a Kaduna, kakakin kungiyar, Kwamared Mujaheed Amin-Modibbo, ya ce:

“Sanata Bala ya nuna halaye na kwarai na nagartaccen shugaba tun lokacin da ya fara siyasa a Najeriya tun daga asalinsa, a matsayin minister a FCT sannan a matsayin Gwamna na yanzu na jihar Bauchi.”

Kungiyar ta nemi gwamnan ya tsaya takarar shugaban kasa; yakin neman zabe da karfi, lashe zaben tare "dawo da" martabar kasar.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel