Mamakon Ruwan Sama Ya Cinye Mutum 5, Ya Yi Kaca-Kaca da Gonakin Al'umma 1,567 a Bauchi

Mamakon Ruwan Sama Ya Cinye Mutum 5, Ya Yi Kaca-Kaca da Gonakin Al'umma 1,567 a Bauchi

  • Wani ruwan sama mai tsanani ya lakume rayukan mutun 5 tare da lalata amfanin gonakin mutane a jihar Bauchi
  • Rahotanni sun bayyana cewa ruwan wanda aka shafe sama da awa 20 ana tafkawa ya haifar da ambaliya
  • Shugaban ƙaramar hukumar Jama'are, Jarma, ya tabbatar da faruwar lamarin a yankin da yake jagoranci

Bauchi - Wani ruwan sama mai tsanani da ya haifar da ambaliya ya lalata gonakin mutane akalla 1,567 a karamar hukumar Jama'are, jihar Bauchi, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Mamakon ruwan wanda aka shafe sama da awanni 20 ana yi, ya lalata amfanin gonakin mutane a ƙauyuka 7 dake yankin.

Shugaban ƙaramar hukumar Jama'are, Sama'ila Jarma, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Mutane na kokarin kwashe kayayyakin su yayin ambaliya
Mamakon Ruwan Sama Ya Cinye Mutun 5, Ya Yi Kaca-Kaca da Gonakin Al'umma 1,567 a Bauchi Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewar Jarma, kauyukan da ambaliyar ruwan ya shafa sun haɗa da Jogiyal, Yola, Doko-Doko, Gongo, Kabigel, Digiza da Massalachin Idi duk a yankin karamar hukumar Jama'are.

Menene musabbabin ambaliyar?

Kara karanta wannan

Mutane 10 sun jikkata yayin da sojoji suka dakile wani kazamin rikici a Filato

Shugaban ya bayyana cewa tekun Jos ne ya yi ambaliya biyo bayan wani mamakon ruwa da aka tafka wanda ya shefe awanni ana yi ranar Talata.

Vanguard ta ruwaito a jawabinsa yace:

"Mun gano gawarwaki biyar a cikin ruwa a yankin da ambaliyar ta shafa. Ɗaya daga cikin gawar daga kauyukan da lamarin ya shafa ya fito yayin da har yanzun ba'a gano asalin sauran mutum 4 ba."
"Mun rika mun binne gawarwakin bayan mun yi iyakar yin mu mugano inda mutanen suka fito. Amma mun ɗauki hotunansu ya Allah wasu zasu zo nema."

Wane mataki gwamnati ta ɗauka?

Jarma ya kara da cewa gwamnatinsa ta kaddamar da kwamitin da zai binciko asarar da aka yi domin mika wa gwamnatin jiha ta ɗauki mataki.

A jawabinsa yace gwamnatinsa ta raba kayan abinci da sauran abubuwan rayuwa domin rage raɗaɗi kafin gwamnatin jiha ta shigo cikin lamarin.

An tafka ruwan da ba'a taba irinsa ba cikin shekara 100

Kara karanta wannan

An Tafka Ruwan Sama a Rana Daya da Ba'a Taba Irinsa Ba Cikin Shekara 100 a Katsina

A wani labarin kuma kun ji cewa An Tafka Ruwan Sama a Rana Daya da Ba'a Taba Irinsa Ba Cikin Shekara 100 a Katsina

Shugaban hukumar Hasashen yanayi ta kasa, Farfesa Mansur Bako Matazu, shine ya bayyana haka a wani taro da NiMet ta shirya a Abuja .

A cewar shugaban NiMet yawan ruwan da aka samu shine kololuwar ruwan da aka taɓa yi a jihar cikin shekara 100, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262