Zamu Kawo Karshen Ayyukan Ta'addanci a Shekarar 2022, Gwamna Zulum

Zamu Kawo Karshen Ayyukan Ta'addanci a Shekarar 2022, Gwamna Zulum

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya bayyana cewa insha Allahu za'a kawo karshen ta'addanci a 2022
  • Gwamnan ya faɗi hakane yayin da yakai wata ziyarar bazata babban asibitin garin Monguno
  • Zulum ya yi alƙawarin inganta asibitin ta hanyar ɗaukar karin ma'aikata da gina musu gidaje

Borno - Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa da izinin Allah za'a kawo karshen ayyukan ta'addaci da ya addabi mutanen jihar zuwa shekara mai kamawa 2022.

Gwamna Zulum ya faɗi wannan magana ne yayin da yakai ziyara garin Monguno domin duba yadda aikin gina babban asibitin garin ke tafiya.

Hare-haren yan ta'addan ƙungiyar Boko Haram ya lakume rayukan dubban mutane da kuma tilastawa wasu guduwa domin tsira da rayuwarsu a cikin shekaru 12.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum
Zamu Kawo Karshen Ayyukan Ta'addanci a Shekarar 2022, Gwamna Zulum Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Gwamna Zulum ya dakatar da alabashin ma'aikata

Gwamnan ya tarad da wasu ma'aikatan lafiya ba su zo aiki ba a ranar Laraba da yakai ziyarar, kamar yadda dailytrust Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya kai ziyara garin Baga, ya ba talakawa sama da 4000 tallafin kudi

Ba tare da ɓata lokaci ba Zulum ya bada umarnin dakatar da albashin waɗanda sukanyi fashi sannan ya bada umarnin karin albashi ga waɗanda suke zuwa aiki.

A jawabin da yayi a asibitn Zulum yace:

"“Duk ma’aikatan lafiyan da suka cancanta za su samu karin kashi na albashinsu daga yanzu zuwa shekara daya mai zuwa, lokacin da ake sa ran ta’addanci ya kau."

Zamu kara ɗaukar ma'aikata

Gwamna Zulum ya kuma ɗauki alkawarin cewa gwamnatinsa zata kara ɗaukar sabbin ma'aikatan lafiya a asibitin na garin Monguno.

Hakazalika Zulum ya yi alƙawarin gina sabbin gidaje 15 waɗanda za'a baiwa ma'aikatan su ji daɗin aikinsu yadda ya kamata.

A ɓangarensa, shugaban asibitin Monguno, Isa Akinbode, ya koka wa Zulum cewa suna fuskantar karancin ma'aikata da rashin dakin gwaje-gwaje a asibitin.

A wani labarin kuma Ba Zamu Taba Yafe Muku Ba, Martanin Yan Najeriya Ga Kwamandojin Boko Haram da Suka Tuba

Sama da kwamandoji 100 ne suka tuba suka mika makamansu ga sojojij Operation Haɗin Kai na rundunar sojin kasa.

Kara karanta wannan

Farfesa Zulum ya shiga aji kwatsam, ya yi wa Malamai gwaji domin auna kaifin basirarsu

Manyan yan ta'addan sun mikamakansu domin rungumar zaman lafaya tare da neman yan Najeriya su yafe musu kuskuren da suka yi a baya.

Wannan matakin tuba da yan Boko Haram suka ɗauka da kuma shirin da gwamnatin tarayya take yi na canza musu tunani su koma cikin jama'a tare da mutane ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262