Wutar kendir ta haddasa gagarumar gobara, ta lamushe gidaje 30 a Ribas

Wutar kendir ta haddasa gagarumar gobara, ta lamushe gidaje 30 a Ribas

  • Wutar kyandir tayi sanadiyyar asarar gidaje akalla 30 da sauran dukiyoyi masu kimar miliyoyi a wuraren Okwelle na Mile 2 a Port Harcourt
  • An tattara bayanai akan yadda wata mata ta bar kyandir a kunne wanda yayi sanadiyyar kazamar gobarar wacce ta fara tun karfe 6:30am
  • Matasan anguwar sun taru suna amfani da ruwa da omo don kokarin kashe wutar kafin motar kwana-kwana ta iso ta kashe wutar

Rivers - Kyandir ya yi dalilin gobarar datayi sanadiyyar kone gidaje fiye da 30 da dukiyoyi masu kimar miliyoyi a wuraren Okwelle dake Mile 2 a Port Harcourt.

Kamar yadda The Nation ta wallafa, an tattara bayanai akan yadda wata mata ta bar kyandir a kunne wanda yayi sanadiyyar wata kazamar gobara wacce tun karfe 6:30 na safe take ci.

Wutar kendir ta haddasa gagarumar gobara, ta lamushe gidaje 30 a Ribas
Wutar kendir ta haddasa gagarumar gobara, ta lamushe gidaje 30 a Ribas. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Yaya wannan kazamar gobara ta faru?

Mun tambayesu ba’asin wutar sai suka ce wata ce ta kunna kyandir tun karfe 6am wutar take ci sai da ko ina ya cinye. Shiyasa kaga duk an taru.

Kara karanta wannan

Rigima ta kaure a dangi yayin da wata mata ta saida wa saurayinta jaririyar ‘yaruwarta

Ina nan da yarana muna kokarin ganin mun kashe wutar. Sannan mun ga ‘yan kwana-kwana shine muku turasu Okwelle don su kawo dauki. Yanzu haka suna kokarin kashe wutar.

Me ganau suka ce kan gobarar?

Wani mazaunin yankin, Christain Alali ya ce wutar ta kara ruruwa ne sanadiyyar irin kayan alatun da suke cikin gidajen, The Nation ta ruwaito.

A cewarsa:

Kasan akwai katako da yawa a wurinnan. Kafin masu kashe wuta su iso gaba daya gine-ginen sun kurmushe.
Idan ba don masu gadin nan ba da matasa, da kafin masu kashe gobarar su iso komai ya gama lalacewa.

Wata mazauniya yankin ta bayyana yadda komai nata ya kone kuma ta roka gwamna Nyesom Wike ya tallafa musu.

A karon farko, tsohon Gwamna Dickson ya magantu kan tuhumarsa da EFCC take yi

Tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson yace hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta tsitsiye shi sakamakon zarginsa da take da waskar da N17.5 biliyan da kuma karantsaye ga bayyana kadarori.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun damke babban limamin IPOB da layu tare da harsasai

Premium Times ta ruwaito yadda EFCC ta kira Dickson hedkwatarta dake Abuja kan zargin rashawa, amma a lokacin babu cikakken bayani kan yadda al'amuran suka faru.

A yayin bayani kan arangamarsa da EFCC a wata takarda da ya fitar a ranar Talata, Dickson yace an gayyacesa tun makonni biyu da suka gabata kan wani koke da wata kungiyar ta kaiwa EFCC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel