Rigima ta kaure a dangi yayin da wata mata ta saida wa saurayinta jaririyar ‘yaruwarta

Rigima ta kaure a dangi yayin da wata mata ta saida wa saurayinta jaririyar ‘yaruwarta

  • Ana zargin wata mata da sace karamar yarinya, ta saida wa Saurayinta a Enugu
  • Chinaza Okoh tamkar uwa ta ke a wajen wannan Baiwar Allah da ta yi gaba da ita
  • Jami’an tsaro sun bukaci a biya kudi kafin su nemo inda aka kai wannan yarinya

Enugu - Rikici ya na neman ya barke a cikin dangi bayan da wata mata mai suna Chinaza Okoh ta sace wata karamar yarinya, Chisom Adumike a jihar Enugu.

Jaridar Punch ta kawo rahoto a ranar Laraba, 11 ga watan Agusta, 2021, ta ce wannan lamari ya auku ne a Amankwu Olikwu Awgu, karamar hukumar Awgu.

Ana zargin Chinaza Okoh ta dauke wannan jaririya da ke tamkar ‘diya a hannunta, ta saida ta ga saurayinta.

Kamar yadda jaridar ta samu labari, wannan mata da ake zargi, Okoh ta dauke Chisom Adumike ne yayin da ta ke dawo wa daga makaranta a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

EFCC ta cafke yaro da mahaifiyarsa wacce ya tsoma a harkar damfara ta yanar gizo

Wani matashi a kauyen Amankwu Olikwu Awgu, Sunday Nwafor, ya shaida wa manema labarai cewa jami’an tsaro sun yi ram da goggon yarinyar, Misis Okoh.

Jagoran matasan kauyen ya ce maganar ta kai gaban jami’an ‘yan sanda na karamar hukumar Awgu da nufin su yi bincike, su gano yadda jaririyar ta salwanta.

Gwamnan jihar Enugu
Gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

Yadda abin ya faru

Majiyar ta ce an sace Chisom a ranar 28 ga watan Yuli, 2021, bayan an kai ta makaranta har yamma, a lokacin da ya kamata ta dawo gida, sai ba a gan ta ba.

Daga nan aka rika bi gida zuwa gida domin gano wannan yarinya, amma aka neme ta aka rasa. A nan ne aka samu labarin an gan ta tare da Chinaza Okoh.

“Muka laluba ko ina, ba mu ganta ba, washegari mu ka cigaba da nema, sai mu ka lura Chinaza ta na yin wasu kiraye-kiraye da ba a gane kansu ba a waya.”

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta yi magana kan shirin sakin manyan kwararrun masu hada bama-bamai na Boko Haram

“Kafin nan sai aka ji Chinaza Okoh ta ba wata mata shawarar ta saida ‘danta domin ta samu kudin da za ta yi dawainiyar sauran 'ya 'yan, sai aka kira ‘yan sanda.”

Asiri ya tonu, amma an ce sai an kawo kudi

“Da aka kama ta da farko, ta musanya zargin, ta ce ba ta san komai ba, daga baya ta amsa cewa ta mika ta ga wani saurayinta a Mmaku, Micheal Chukwuobasi da wani Anioke Ikechukwu."

Mista Nwafor ya ce har yanzu ba a yi nasarar gano inda aka kai karamar yarinyar ba domin ‘yan sanda sun bukaci sai iyayen yarinyar sun kawo akalla N600, 000.

A makon nan ne aka ji cewa Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya shirya wa wasu malamai jarrabawar ba-zata da rana tsaka da ya ziyarci garin Baga.

Bayan sakamakon jarrabawar ya fito, Babagana Umara Zulum ya raba wa malaman kudi da shaddoji.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Wani ya yi wuf da jarumar fina-finan Hausa, Diamond Zahra

Asali: Legit.ng

Online view pixel