A karon farko, tsohon Gwamna Dickson ya magantu kan tuhumarsa da EFCC take yi

A karon farko, tsohon Gwamna Dickson ya magantu kan tuhumarsa da EFCC take yi

  • Dickson yace wata kungiya ce ta kaiwa EFCC korafi kan zarginsa da waskar da N17.5 biliyan na shawo kan ambaliyar ruwa
  • Akwai wani zargi kuma na kin bayyana wata kadararsa wacce hakan yayi karantsaye ga dokokin bayyana kadarori
  • Tsohon gwamnan yace bai san da batun wadannan makuden kudade ba domin ba a bayyana ta inda suka fito ba balle ya lashe

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson yace hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta tsitsiye shi sakamakon zarginsa da take da waskar da N17.5 biliyan da kuma karantsaye ga bayyana kadarori.

Premium Times ta ruwaito yadda EFCC ta kira Dickson hedkwatarta dake Abuja kan zargin rashawa, amma a lokacin babu cikakken bayani kan yadda al'amuran suka faru.

A karon farko, tsohon Gwamna Dickson ya magantu kan tuhumarsa da EFCC take yi
A karon farko, tsohon Gwamna Dickson ya magantu kan tuhumarsa da EFCC take yi. Hoto daga thenationng.net
Asali: UGC

A yayin bayani kan arangamarsa da EFCC a wata takarda da ya fitar a ranar Talata, Dickson yace an gayyacesa tun makonni biyu da suka gabata kan wani koke da wata kungiyar ta kaiwa EFCC.

Kara karanta wannan

Kungiyar dalibai ta NANS ta kai kukan ta ga Sheikh Gumi da Buhari kan sace dalibai

Yace an gayyacesa ne domin yayi karin bayani kan wasu kadarori amma ya bukaci a sake saka masa wani lokaci, hakan ne yasa ya fada Talata.

Dickson ya nuna mamakinsa a yayin da aka tunkaresa da zargin waskar da makuden kudaden amma kuma ba a rubuto su a gayyatar EFCC din ba.

Bayani kan zargin waskar da kudin shawo kan ambaliyar ruwa

Kamar yadda yace, hukumar ta zargesa da amfani da kudin wurin kamfen din sake zabensa a shekarar 2019.

Amma bayan isa ta hukumar, tawagar binciken ta riske ni da sabon zargi na kwashe kudin da aka ware domin shawo kan ambaliyar ruwa har N17.5 biliyan. Korafin ya kara da zargin cewa an yi amfani da kudin wurin kamfen a 2019. A gaskiya babu maganar wadannan kudaden a ambaliyar ruwa da aka dinga samu a Bayelsa a 2012.
Ko a korafin, ba a bayyana wanda ya bada kudin ba ko daga inda suka fito. Haka kuma babu wani batun zarcewa ta Bayelsa a 2019 wanda hakan ya nuna cewa korafin kirkirarre ne.

Kara karanta wannan

Abin kunya ne a ce Buhari dan Arewa ne, 'yan Arewa sun soki mulkin Buhari

Zargin rashin bayyana kadarori

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, Dickson yace batun bayyana kadarori kuwa yana da alaka da wasu hannun jari na iyalinsa wanda ya saka wani bangare a yayin da yake majalisar wakilai.

Yace sunan kamfanin Seriake Dickson Trust wanda ya hada domin tsare iyalansa kuma an saka hannun jarin ne a tsakanin 1996 da 2012 kafin ya zama gwamna.

A yayin tsame kanshi daga yin wani laifi, yace wannan kamfanin da hannayen jarin an kafa su ne da basussuka kuma an hada da alawus, albashi da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel