Ku cire ni daga rikicin shugabancin APC – Tsohon Shugaban jam’iyyar Oshiomhole
- Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adam Oshiomhole, ya nesanta kansa daga zargin shirya makarkashiya don dawowa kujerarsa
- Oshiomhole ya jadadda biyayyarsa ga kwamitin rikon kwarya da Gwamna Mai Mala Buni ke jagoranta
- Ya kuma sha alwashin daukar mataki don hana ambatan sunansa a cikin wani lamari da bai da hannu a ciki
Tsohon Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya musanta shirin komawa kan kujerarsa.
Ya nisanta kansa daga rikicin shugabanci da ke girgiza jam’iyyar mai mulki, jaridar The Nation ta ruwaito.
Oshiomhole, a cikin wata sanarwa a Abuja a ranar Laraba, 11 ga watan Agusta ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Victor Oshioke, ya bayyana hasashen a matsayin karya.
Ya sake tabbatar da biyayyarsa ga APC karkashin jagorancin Gwamna Mai-Mala Buni.
Tsohon gwamnan na Edo ya nisanta kansa daga wata sanarwa da aka alakanta ga Cif Eze Chukwuemeka Eze, mai kiran kansa mai taimaka wa wani Minista daga Kudu maso Kudu ya nakalto cewa Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da aikin yi, da sauran su suna shirya munakisa don dawowar Oshiomhole ofis.
Tsohon Shugaban na APC ya ce maganar ba gaskiya bace, inda ya tuno irin rawar da Keyamo ya taka wajen rushe Kwamitin Aiki na jam’yyar na Kasa (NWC) a shekarar 2020.
Oshiomhole ya tuno cewa Keyamo shine kan gaba kuma ya ba da goyon bayan doka ta hannun mataimakansa na shari'a a kotu kuma yayi jayayya a madadin wadanda suka shigar da kara don cire shi.
Tsohon shugaban ya ce ba zai kasance cikin duk wani shiri na kawo rudani ko yin izgili ga jam'iyyar ta kowace hanya ba ko saboda wani dalili.
Ya jaddada cewa ya dauki kwararan mataki don ganin ba a sanya sunansa cikin wani batun da ba shi da hannu a ciki ba, PM News ta ruwaito.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“Wannan wata dama ce ta kara tabbatar da biyayyar Kwamared Adams Oshiomhole ga jam’iyyar APC a karkashin kyakkyawar jagorancin Mai Girma Gwamna Mai-Mala Buni.
"Matsayin Oshiomhole shi ne cewa dukkan a hada hannu don tallafawa kwamitin rikon kwarya da Gwamna Mai-Mala Buni ke jagoranta wajen kammala aikinsa maimakon haifar da abubuwan da ba su dace da aikin kwamitin ba.
"Yana taya Gwamna Mai Mala Buni da daukacin membobin Kwamitin rikon kwarya murna kan kokarinsu na rage darajar gwamnonin PDP ta hanyar lashe uku daga cikinsu zuwa APC."
A wani labarin kuma, dubbannin mambobin jam'iyyar APC mai mulki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta YPP a jihar Kwara, kamar yadda the nation ta ruwaito.
This day ta rahoto cewa, kungiyar waɗanda suka sauya shekar da ake kira 'Third Force' (KSTF) sun bayyana cewa dalilin rikicin APC yasa suka fice daga cikinta.
Hakanan sabbin mambobin YPP ɗin sun sha alwashin kwace mulki daga hannun APC a jihar a babban zaɓen 2023 dake tafe saboda kusoshin tafiyar O to Ge sun koma YPP.
Asali: Legit.ng