Rikicin cikin gidan PDP ya kara kamari, Mataimakan Secondus sun juya masa baya
- Taofeek Arapaja da wasu manyan PDP sun bukaci Uche Secondus ya yi murabus
- Mataimakan shugabannin jam’iyyar suna cikin masu huro masa wutan ya sauka
- Ambasada Arapaja ya ce idan Secondus ya na nan, PDP ba za ta iya kai labari ba
Wasu daga cikin mataimakan shugaban jam’iyyar PDP na kasa, sun yi kira ga Prince Uche Secondus ya yi murabus daga kan kujerar da yake kai.
Taofeek Oladejo Arapaja sun yi wa Secondus taron dangi
Jaridar Punch ta ce wadanda suka dauki wannan mataki sun hada da mataimakan shugaban PDP na shiyyar Kudu maso yamma, Taofeek Oladejo Arapaja.
Sauran su ne Dan Osi, Ali Odefa da Dankus Shau wanda su ne mataimakin shugabannin PDP na Kudu maso kudu, Kudu maso gabas da Arewa ta tsakiya.
Rahoton ya ce shugabannin jam’iyyar adawar sun bayyana wannan a wani jawabi da suka fitar a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, 2021, a birnin tarayya Abuja.
Mai taimaka wa Ambasada Taofeek Oladejo Arapaja wajen yada labarai, Ibrahim Bamitale, ya fitar da jawabin a jiya, ya na kira ga shugaban PDP ya sauka.
Shugabannin jam’iyyar ta PDP sun yi kira ga magoya baya su kwantar da hankalinsu, amma suka ce ya kamata shugaban jam’iyyar ya sauka daga kujerarsa.
Jawabin shugabannin jam'iyyar PDP na kasa
“Domin ceton jam’iyya daga karin matsaloli, mataimakan shugaban jam’iyya sun shirya taron gaggawa a Abuja a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, 2021, domin duba halin da ake ciki, aka yanke cewa:
“Shugaban jam’iyya na kasa, Prince Uche Secondus, ya yi murabus, ya ceci jam’iyyar daga cigaba da barkewar da ake fuskanta a halin yanzu.”
“Murabus din shugabannin PDP ya zo ne a dalilin gazawar shugaban jam’iyya na hana wasu gwamnoni sauya-sheka zuwa jam’iyya mai mulki da ta gaza.”
Da aka tuntubi Taofeek Oladejo Arapaja, sai ya ce kan jam’iyya ya rabu, ba za ta iya cin zabe muddin Prince Uche Secondus ya na nan ba, dole ya tafi kafin 2023.
Babu zaman lafiya a APC
A bangare guda kuma, rikicin APC ya ki lafa wa a Zamfara, shugaban jam’iyya na rikon kwarya ya yi wa tsohon Gwamna, Ahmad Sani Yariman-Bakura raddi a jiya.
Kalaman Jigon Jam’iyya, Yariman-Bakura suna neman tada sabuwar rigima a APC bayan ya ce dole sai kowane 'dan jam'iyya ya sabunta rajistarsa a jihar Zamfara.
Asali: Legit.ng