Rikicin Siyasa: Mambobin Kwamitin Zartarwa Sun Tsige Shugaban Jam'iyyar APC

Rikicin Siyasa: Mambobin Kwamitin Zartarwa Sun Tsige Shugaban Jam'iyyar APC

  • Yan kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC a jihar Enugu sun kaɗa kuri'ar tsige shugaban APC na jihar
  • Kwamitin ya zargi tsohon shugaban da nuna rashin ɗa'a da kuma fatali da dokokin APC wajen gudanar da gangami
  • Kwamitin mai mambobi 42 ya amince da naɗin mataimakinsa a matsayin shugaban riko na APC a jihar

Enugu - Mambobin kwamitin zartarwa (SEC) na jam'iyyar APC reshen jihar Enugu sun tsige shugaban jam'iyyar, Dr. Ben Nwoye, daga mukaminsa

Leadership ta rahoto cewa mambobin sun ɗauki wannan matakin ne bisa zarginsa da kokarin tarwatsa jam'iyyar APC a jihar.

Daga nan ne suka naɗa mataimakin shugaban, Prince Chikwado Chukwunta Nnaji, a matsayin shugaban APC a Enugu na rikon kwarya.

An tsige shugaban APC na jihar Enugu
Rikicin Siyasa: Mambobin Kwamitin Zartarwa Sun Tsige Shugaban Jam'iyyar APC Hoto: blueprint.ng
Asali: UGC

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da kwamitin mai mambobi 42 ya fitar ɗauke da sanya hannunsu ranar Talata.

Wane dalili yasa aka tsige shugaban?

Kwamitin zartarwa ya zargi tsohon shugaban da nuna halin rashin ɗa'a da yin fatali da shinfiɗaɗɗen tsarin gudanar da gangamin taron APC wanda kwamitin rikon kwaryar APC ta kasa ya samar.

Kara karanta wannan

Rikicin gida: APC ta dauki matsaya, ta bukaci Mala Buni ya shirya zaben shugabanni da wuri

Hakanan kwamitin ya zargi tsohon shugaban da ƙin yin amfani da kundin tsarin mulkin APC wajen jagorancinsa, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban rikon kwarya, Prince Gilbert C. Chukwunta, yace:

"Mambobin kwamiti sun haɗu domin ceto jam'iyyar mu daga rugujewa matukar Nwoye ya cigaba da jagorancin jam'iyyar APC a jihar."

Waɗanda suke tare da shi yayin wannan jawabin sun haɗa da sakatare, Chief Robert Eze, da shugabar mata, Hon Mrs Oby Nwofor.

Sauran sun haɗa da shugaban matasan APC na jihar, Joshua Mamah, da kuma sakataren kuɗi, Dr. Mrs. Amaka Adonu.

A wani labarin kuma Babban Malamin Addini Ya Kwace Matar Dalibinsa Daga Zuwa Neman Albarkar Aure

Wani mutumi, Bright Ben, ya zargi babban faston cocin su ta General Overseer dake Eneka, karamar hukumar Obio-Akpor, jihar Rivers da yi masa kwacen mata.

Bright ya bayyana cewa lamarin ya fara ne daga lokacin da aka baiwa matarsa da sukai shekara 12 tare mukamin mai hidima ga coci.

Kara karanta wannan

Bayan Fitowa Daga Taro, Gwamnonin APC Sun Bayyana Matakin da Suka Dauka a Kan Shugaban APC Mai Mala Buni

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262