Rikicin gida: APC ta dauki matsaya, ta bukaci Mala Buni ya shirya zaben shugabanni da wuri

Rikicin gida: APC ta dauki matsaya, ta bukaci Mala Buni ya shirya zaben shugabanni da wuri

  • Gwamnonin Jam’iyyar APC sun yi taro na musamman a birnin tarayya Abuja
  • PGF ta gamsu da halaccin kwamitin rikon kwarya na Gwamna Mai Mala Buni
  • Kungiyar gwamnonin ta bukaci kwamitin ya gaggauta yin zabukan Jam’iyya

Abuja - Gwamnonin da ke karkashin jam’iyyar APC mai mulki sun bukaci kwamitin Gwamna Mai Mala Buni ya yi maza ya gudanar da zaben shugabanni.

Daily Trust ta ce gwamnonin sun ba kwamitin rikon kwarya ya shirya babban gangami da umarni ya shirya zabukan kananan hukumomi, jihohi da ma na kasa.

Hakan ya zo ne a cikin wani jawabi da shugaban gwamnonin APC, mai girma gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Abubakar Bagudu ya fitar a ranar Talata.

Mecece matsayar Gwamnonin APC a kan kwamitin Buni?

Jaridar ta ce kungiyar PGF ta gwamnonin APC sun nuna cikakken goyon bayansu ga a kwamitin rikon kwayar, suna mara masu baya su cigaba da zama a ofis.

Kara karanta wannan

Bayan Fitowa Daga Taro, Gwamnonin APC Sun Bayyana Matakin da Suka Dauka a Kan Shugaban APC Mai Mala Buni

“An yi wa kungiyar bayani game da hukuncin ranar 28 ga watan Yuli, 2021, da kotun koli ta yi a game da shari’ar karar zaben gwamnan jihar Ondo na 2020.”
“An tabbatar da cewa kwamitin rikon kwarya da tsara zaben ya na da gindin zama ta fuskar shari’a.”

Manyan APC
Gwamnonin APC a wani taro Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yajin-aikin kungiyar NARD

Premium Times ta ce gwamnonin sun roki kungiyar manyan likitoci na NARD ta yi hakuri ta janye yajin-aikin da ta shiga, ta yi kira ta saurari sulhun da ake yi.

Atiku Abubakar Bagudu a madadin sauran abokan aikin na sa, ya yi kira da babbar murya ga hukumomin gwamnati da abin ya shafa, su saurari koken likiocin.

PGF ta yi magana a kan zaben mazabun da aka yi?

Jam’iyyar APC ta soma fito da shugabanninta, inda aka yi zaben mazabu a makonnnin da suka wuce. PGF ta ce ta ji dadin yadda wadannan zabukan suka gudana.

Kara karanta wannan

Yunkurin korar Secondus da sauran Shugabannin PDP ya sa Gwamnoni sun rabu zuwa gida uku

A karshe gwamnonin sun roki ‘ya ‘yan jam’iyya su cigaba da bada gudumuwarsu a kowane mataki.

A daidai wannan lokaci ne ake jin wasu mataimakan shugaban jam’iyyar PDP, sun taso Prince Uche Secondus gaba, sun ce dole sai ya yi murabus daga matsayinsa.

A karshe jam'iyyar hamayyar ta ce ba za'a tsige Uche Secondus daga kujerarsa ba, amma za'a gaggauta gudanar da gangami a Oktoba, maimakon karshen shekara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel