Ban ce Maguzawa ne suka kafa jihar Kano ba, cewa nayi akwai Maguzawa yan asalin Kano: Aisha Yesufu

Ban ce Maguzawa ne suka kafa jihar Kano ba, cewa nayi akwai Maguzawa yan asalin Kano: Aisha Yesufu

  • Aisha Yesufu ta yi tsokaci kan maganan da aka ce ta ce Maguzawa sune suka kafa jihar Kano
  • A cewarta mutane basa karatu da fahimta, domin ita cewa tayi akwai Maguzawa ‘yan asalin jihar
  • Ta kalubalanci masu sharhi kan lamarin da su koma su karanci tarihi domin jin yadda lamarin yake kan usulin Maguzawa a jihar

Shahararriyar mai fafutukar nan ta Najeriya, Aisha Yesufu ta yi tsokaci a kan rade-radin da mutane ke yi na cewa ta ce Maguzawa sune suka kafa jihar Kano, lamarin da ya haifar da zafafan martani daga fusatattun mutane.

Kamar yadda muka sani dai Kalmar Maguzawa tana nufin mutane da ke zaune a kasar Hausa amma kuma suke ba Musulmai ba.

Aisha ta jadadda cewa ko shakka babu tarihi ya nuna cewa akwai Maguzawa 'yan asalin jihar Kano wadanda suke su Kiristoci ne tun a zamanin da.

Sai dai ta ce sabanin yadda aka fadi zancen ita cewa tayi babu inda yake a kasar da za a ce an samu 'yan asalin wuri guda kuma ace dukkansu addininsu daya.

Kara karanta wannan

Ba su yarda mata za su iya jagoranci ba, za mu nuna masu kuskurensu: Shugabar Kasar Tanzania ta magantu

Ban ce Maguzawa ne suka kafa jihar Kano ba, cewa nayi akwai Maguzawa yan asalin Kano: Aisha Yesufu
Aisha Yesufu ta ce ita bata ce Maguzawa bane suka kafa jihar Kano
Asali: UGC

A hira da Editan Legit.ng Hausa yayi da ita an jiyo tana cewa:

“Zancen da nayi a kan Twitter na cewa Maguzawa sune a Kano, dama su aka sani a wajen, shine abun da ake kira tarihi mutane basa karanta shi ne ko yaya? Wani abu ma da naji ance na fadi shine wai nace kiristoci ne suka kafa jihar Kano, nace toh a ina kiristoci suka kafa ta tunda addinin Musulunci ya zo kafin kiristanci ya zo nan Kanon.
“Abun da na fada, ana zance ne wani ne yayi zance a kan cewa akwai Musulmai da suke Inyamurai kuma asalinsu Inyamurai ne a chan inda Inyamurai suke. Nace gaba daya Najeriyarnan ba inda yake da za ka hadu ace akwai mutanen da suke da asali wai babu wani addinin da ya banbanta da wadanda suke da yawa.
“Sai na kawo misali nace ko a Kano ma akwai Maguzawa da suke su ba Musulmai bane su Kiristoci ne kuma yan Kano ne, kuma sune ma asalin yan Kanon, abun da na fada kenan. Maganar ba haka yake ba? A Kanon akwai su a Jigawa akwai su, babu inda babu su, yawa ne basu da shi kamar yadda sauran suke. Maganar da nayi kenan, toh ban ga me yasa in aka yi abu daya masu juyawa suyi ta juyawa, masu kawo canfe-canfe suyi ta yi ana fadin abubuwan da bai kamata ba.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun kashe wani bawan Allah, sun nemi a biya miliyan N50 kudin fansar mata da ‘yarsa da suka sace

“Menene a ciki? Magana ne yadda yake kuma an fade shi menene a ciki. Don nace akwai Kiristoci a Kano toh me kenan?
“Ya kamata mutane su dunga karatu da fahimta, shiyasa ko a makaranta lokacin da ake koyon yare, ko Hausa ko Turanci akwai abunda ake kira fahimta, idan ka karanta abu ka fahimci abun da ake nufi ba wai ka karanta don ka bayar da amsa ba. Sannan a cikin wannan yanayin da nayi magana dama ka sa sai na dauko na kalle shi sai na fassara, har sai da nace Kalmar maguzawan wasu suna daukar shi kamar ma kalan zagi ne ma, da na fadi hakan ma sai nace yawancinsu ba Musulmai bane ma Kirista ne, ko suna ganin kamar ba ‘yan Kanon da suke su kirista ne?
“Maguzawan ba sune suke a su Dala da Gauron dutse? Maguzawan ai ba Hausa suke yi ba, kuma ba sune ‘yan asalin Kanon ba? Sannan da Hausawa ai wannan ba wani abun fada bane, a nemi tarihi mana a karanta. Tun ina Sakandare, na fara sakandare a GGSS Kabo tun lokacin akwai ma wata Saratu Musa ‘yar ajinmu ita Bamagujiya ce ‘yar Kano. Mun karanta a tarihi ko kuma suna so su juya tarihi ne, na ga mutane komai suna so su juya shi.

Kara karanta wannan

Asadul-Islam, Datti Assalafy sun yi mun kazafi iri-iri, wasu cewa sukayi mijina ba Musulmi bane: Aisha Yesufu

Kan cewa Kalmar da tayi na cewa Maguzawa ne ‘yan asalin Kano shine ya fusata jama’a, Aisha ta ce:
“Bari ma nayi bayani, ka ga lokacin idan aka tada zance cewa za a yi zaman kwana uku idan aka yi mutuwa, da sadakar bakwai da arba’in, ina jin idan aka ce ba zan manta ba ina jin, ban dai tabbatar ba amma ina jin a bakin Marigayi Mallam Jaafar na fara jin wannan bayanin inda yace lokacin nan Maguzawan sune lokacin nan idan mutum ya mutu suna zama kwana uku, kwanan bakwan nan suna shan su burkutu da giya da sauran. Shine lokacin nan da Musulunci ya zo da suka fara karbar Musulunci sai aka ce toh maimakon zaman nan ana shan su burkutu toh a dunga yi ana hadawa da sadaka ana addu’a.
“Toh inda aka samu wadannan zaman nan kenan inda aka ce bidi’a ne, kuma daga asalin inda abun ya taso kenan amma ya ake magana kamar dama ‘yan Kanon tun asali sun tashi suna Musulmai ne. Ni ko kauyena ni yar Edo ce, kafin ma Turawa su zo su kawo Kiristanci sun tarar da mu da addinin, sun tadda mu da addininmu Musulunci.”

Kara karanta wannan

Karantsaye ga tsaro a gidan gwamnatin Borno: Shugaban wata NGO ya shiga hannun hukuma

Asadul-Islam, Datti Assalafy sun yi mun kazafi iri-iri, wasu cewa sukayi mijina ba Musulmi bane: Aisha Yesufu

A wani labarin, Aisha Yesufu, ya bayyana yadda Musulmai, cikinsu har da Malaman addini ke sukarta kan abubuwan da take yi.

A cewarta, mutane da dama sun yi mata kazafi iri-iri kuma babu abinda za ta ce illa ta bar su da Allah.

A hirar da tayi da wakilin Legit Hausa, Aisha Yesufu tayi tsokaci kan yadda Malamin Addini, Ibn Al-Qasim Asadul Islam, ya ke kokarin haramta abinda Allah ya hallata inda yace mata ta daina sanye Hijabi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel