Asadul-Islam, Datti Assalafy sun yi mun kazafi iri-iri, wasu cewa sukayi mijina ba Musulmi bane: Aisha Yesufu

Asadul-Islam, Datti Assalafy sun yi mun kazafi iri-iri, wasu cewa sukayi mijina ba Musulmi bane: Aisha Yesufu

  • Aisha Yesufu ta yi tsokaci kan maganan masu zarginta da maigidanta
  • A cewarta mutane su mayar da hankali kan halin da yan Najeriya ke ciki na wahala da yunwa
  • Tace duk wanda yayi mata sharri ta bar shi da Allah

Shahrarriyar 'yar fafutuka kuma mai rajin kare hakkin mata, Aisha Yesufu, ya bayyana yadda Musulmai, cikinsu har da Malaman addini ke sukarta kan abubuwan da take yi.

A cewarta, mutane da dama sun yi mata kazafi iri-iri kuma babu abinda za ta ce illa ta bar su da Allah.

A hirar da tayi da wakilin Legit Hausa, Aisha Yesufu tayi tsokaci kan yadda Malamin Addini, Ibn Al-Qasim Asadul Islam, ya ke kokarin haramta abinda Allah ya hallata inda yace mata ta daina sanye Hijabi.

A cewarta, ta wani dalili Malami zai hana mutum abinda Allah ya wajabta masa.

Tace:
"Sa Hijabin da nike, zaka ji mutane suna fitowa suna cewa 'ki daina sa Hijabi, ai ke ba Musulma bace,'."

"Sai kaji Musulmi yace dokar da Allah ya kafa na mace ta rufe kanta amma wani zai ce in ajiye. Har akwai wani Malami yana cewa in ajiye Hijabi, ka ga shirka kenan dokar da Allah ya ajiye shi yana son ya bada nashi dokan."

Da muka tambayeta wani Malami ne yace mata hakan, tace bata san sunansa ba amma ta ga bidiyon da ya fadi hakan.

Tace:

"Ni ban san sunanshi ba, amma yana nan har da bidiyo yayi. Da kannena suka turo min na fara kallo cewa nayi bani da lokaci tunda akwai ranar Hisabi zamu tsaya gaban Allah."
"Duk masu min sharri ko a jikina, ko damuwa bana yi. Ina zan samu lokacinsu bayan mutane na kiranka suna kukan yunwa ba abinci, babu kudin zuwa asibiti."

Asadul-Islam, Datti Assalafy sun yi mun kazafi iri-iri, wasu cewa sukayi mijina ba Musulmi bane: Aisha Yesufu
Asadul-Islam, Datti Assalafy sun yi mun kazafi iri-iri, wasu cewa sukayi mijina ba Musulmi bane: Aisha Yesufu
Asali: UGC

Ta turo mana bidiyon hakan

Daga baya da ta turo mana bidiyon, mun gano cewa Malamin da yayi magana, Sheikh Bn Al-Qasim Asadul-Islam ne, yayinda yake mata raddi kan kiran da tayi ga Ministan sadarwa, Malam Isah Pantami, ya sauka daga kujerarsa.

Game da mijinta kuwa, tace ta samu labarin cewa an ce ba Musulmi bane. Hakazalika sun ce ya wawura kudin gwamnati lokacin da yayi aiki a NHIS.

A bayanin da tayi, tace wannan ba gaskiya bane.

Tace:

"Kwanaki wani ya kira kanwata yace yaji mijina ba Musulmi bane. Tace 'Inna Lillahi wa inna ilaihi raji'un, ina kaji wannan maganan?' Ni kuma nace tun yaushe suna fada, tsakani da Allah nike abu ba don mutum ba. Abin tsoro shine Allah."
"Kwanaki akace maigidana ya saci kudi a NHIS. Nace shi kanshi ya san ni zansa akaishi kurkuku a rufe in ya saci kudi. Wani mutumi ne dan Katsina mai suna Usman Yusuf, kuma ba sunan mai gidana ba kenan."

Daga baya ta turo mana jawabin Datti Assalafy inda yace mijinta ba Musulmi bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel