Karantsaye ga tsaro a gidan gwamnatin Borno: Shugaban wata NGO ya shiga hannun hukuma

Karantsaye ga tsaro a gidan gwamnatin Borno: Shugaban wata NGO ya shiga hannun hukuma

  • An kama wani Santiago Alexander da direbansa sakamakon yin karantsaye ga tsaron gidan gwamnatin jihar Borno
  • Duk da dai jami’an tsaron gidan gwamnati sun dakatar da motar amma sam taki tsayawa ta nufi hanyar gidan Zulum gadan-gadan
  • An nemi duk wata alama wacce za ta bayyana ko wanene shi amma sam babu a tare dashi, tuni ‘yan sanda suka damkesu

Maiduguri, Borno - An kama wani Santiago Alexander, dan kasar waje wanda yace shi shugaban kungiya mai zaman kanta ne ta ACTED, bisa yin karantsaye ga dokar tsaro na gidan gwamnatin jihar Borno dake Maiduguri kamar yadda TheCable ta ruwaito.

TheCable ta gano yadda aka kama Santiago da misalin karfe 4pm a cikin wata mota mai kalar toka kirar Sienna mai lamba ta MAG 479 RM.

Karantsaye ga tsaro a gidan gwamnatin Borno: Shugaban wata NGO ya shiga hannun hukuma
Karantsaye ga tsaro a gidan gwamnatin Borno: Shugaban wata NGO ya shiga hannun hukuma. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Santiago da direbansa sun nufi gidan Zulum kai tsaye

Santiago, wanda ba a gane dan wacce kasa bane ya nufi gidan gwamna Babagana Zulum ba tare da wata alama da za a gane shi da ita ba aka dakatar dashi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa ba za ta tattauna da 'yan bindiga ba

Direban Santiago mai suna Abubakar Suleiman bashi da wata alama da za a gane ko shi wanene a tare da shi.

Wanda ake zargin a cewarsa ya yi kokarin zuwa wani dakin taro ne na JPB da NC akan ayyukan cigaba amma kuma ya tafi gidan gwamnati.

Inda direban yace zasu je kusan nisan kilomita daya ne kuma ga alamu nan sarai da suke nuna cewa inda suka ce zasu je da bambamci da inda suka nufa.

Jami’an tsaro sun yi zargin akwai lauje a cikin nadi bayan an yi ta dakatar da motarsu amma suka yi kunnen uwar shegu dasu. Sai da jami’an tsaro suka bisu da gudu kafin suka samu nasarar dakatar dasu.

An kara zarginsu bayan akwai alamu da dama na rubuce-rubuce da sauran hanyoyin da mutum zai gane inda suka ce zasu je da babu yanda za a yi a kasa gane wurin.

Santiago yace wani ya je gani a wurin taro

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Kutsa Wurin Ibada Sun Hallaka Babban Malami Yana Tsaka da Addu'a

Bayan an tambayi Santiago, wanda ba a gayyaceshi zuwa gidan gwamnati ba, ya ce an aike shi ya kai sakone zuwa wurin wani Oluseyi Fatuyi na bangaren hadin kan kasa da kasa dake karkashin ma’aikatar kudi dake a Maiduguri don yin taron JTB na kwana uku.

Fatuyi ya amsa cewa tabbas sun yi zasu hadu da Santiago.

Zulum ya umarci kwamishinan ‘yan sanda ya mayar da hankali wurin cigaba da bincike akan lamarin.

Nasara daga Allah: 'Yan Boko Haram 88 sun mika wuya da makamansu ga sojojin Najeriya

Sakamakon bude wutar da Operation Hadin Kai suke yi wa ‘yan Boko Haram, tuni ‘yan ta’addan da iyalansu suka fara mika wuya ga sojoji suna zubar da makamansu, prnigeria ta wallafa.

‘Yan Boko Haram wadanda suka zagaye dajin Sambisa bayan sun ji aman bama-bamai daga sojin sama dana kasa sun nufi sansanin sojoji na Forward Operational Base (FOB) dake Banki Junction/BOCOBS a Bama dake jihar Borno a ranar 2 ga watan Augustan 2021.

Kara karanta wannan

Yadda aka tsinci gawar wani jami'in JTF a karkashin gada a Abuja

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: