FG ta kira jakadan Najeriya, tayi barazanar sake duba alakarta da Indonisiya bayan cin zarafin jami’inta

FG ta kira jakadan Najeriya, tayi barazanar sake duba alakarta da Indonisiya bayan cin zarafin jami’inta

  • Gwamnatin tarayya ta dauki kwararan matakai kan harin da jami’an shige da fice na Indonesiya suka kaiwa jami’in diflomasiyyar Najeriya
  • Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama ya ce an kira jakadan Najeriya a Indonesia don tattaunawa
  • Ministan ya kuma ce bayan hakurin da jakadan Indonesiya a Najeriya ya bayar, dole ne a hukunta jami'an hukumar shige da ficen

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake duba alakarta da Indonesiya bayan harin da jami’an shige da fice na kasar suka kaiwa jami’in diflomasiyyar Najeriya.

Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, ya bayyana hakan a wani taro da aka gudanar a Abuja a ranar Talata, 10 ga watan Agusta.

FG ta kira jakadan Najeriya, tayi barazanar sake duba alakarta da Indonisiya bayan cin zarafin jami’inta
Gwamnatin tarayya tayi barazanar sake duba alakarta da Indonisiya bayan cin zarafin jami’inta Hoto: Ministry of Foreign Affairs, Nigeria
Asali: Facebook

Onyeama ya kuma ce an gayyaci jakadan Najeriya a Indonesia don ci gaba da tuntuba da kuma bayar da cikakken bayani kan harin.

Legit.ng ta bayyana cewa takaitaccen bayanin Onyeama ya biyo bayan la'antar da ma'aikatar ta yi a baya game da harin wanda aka nada a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Kungiyar dalibai ta NANS ta kai kukan ta ga Sheikh Gumi da Buhari kan sace dalibai

Dole ne a dau mataki kan jami’an da abun ya shafa

Tun farko ma'aikatar harkokin waje ta ce jakadan Indonesiya a Najeriya ya nemi afuwa kuma jami'an shige da fice da abin ya shafa suma sun ziyarci ofishin jakadancin Najeriya da ke Indonesia don neman afuwar jami'in diflomasiyyar.

Sai dai Onyeama ya ce gwamnatin tarayya na son gwamnatin Indonesiya ta dauki kwakkwaran mataki.

Ya sake nanata cewa dole ne a sanya wa jami’an da ke da hannu cikin wannan takunkumi.

An kuma sake bayyana matsayin Onyeama a cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatar harkokin waje Esther Sunsuwa ta sanya wa hannu, kuma aka fitar jim kadan bayan kammala taron manema labaran.

Buratai Ya Gana da Shugaban Kasar Benin, Inda Ake Shari'ar Sunday Igboho

A wani labari na daban, jakadan Najeriya a Benin, Tukur Yusuf Buratai, ya gana da shugaban ƙasar, Patrice Talon.

Buratai ya gana da shugaban ne domin gabatar da kansa da takardar fara aikinsa a matsayin jakadan Najeriya a Benin.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta

A kwanakin baya shugaban ƙasa ya bayyana naɗa Buratai a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar jamhuriyar Benin, kamar yadda punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel