Sabon Rahoto: Jerin Manyan Masu Kudin Duniya, Dangote Ya Koma Na 117 a Duniya

Sabon Rahoto: Jerin Manyan Masu Kudin Duniya, Dangote Ya Koma Na 117 a Duniya

  • Babban attajirin nan na Najeriya da Africa, Aliko Dangote, ya koma na 117 a jerin manyan attajiran duniya da aka fitar
  • Rahoton wanda jaridar Bloomberg ta fitar ya nuna cewa Dangote ya mallaki dala biliyan $17.8bn
  • Elon Musk, shine attajirin da yafi kowa kuɗi a duniya kamar yadda rahoton ya nuna da dala biliyan $194bn

Kano - Sabon rahoton manyan attajiran duniya da jaridar Bloomberg ta fitar ya nuna cewa attajirin mai kuɗin Najeriya, Aliko Dangote ya koma na 117.

Kafin fitar da rahotonta, jaridar Bloomberg tana bincike da tattara bayani tare da lissafa dukiyar da kowane mai kuɗi ya mallaka.

BBC Hausa ta ruwaito cewa Bloomberg na yawaita fitar da rahoto game manyan mafiya arziki a duniya.

A wannan karan rahoton ya bayyana cewa Aliko Dangote, shugaban kamfanin 'Dangote Group' ya mallaki dukiyar da takai dalar Amurka biliyan $17.8bn.

Aliko Dangote
Sabon Rahoto: Jerin Manyan Masu Kudin Duniya, Dangote Ya Koma Na 117 a Duniya Hoto: time.com
Asali: UGC

Wanene yafi kowa arziki a duniya?

Wanda yafi kowa kuɗi a duniya a cewar rahoton shine Elon Musk, haifaffen ƙasar Africa ta kudu, wanda ya mallaki dalar Amurka biliyan $194bn.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Zazzabin cizon sauro yana kashe yan Najeriya 9 a kowane minti 60, Minista

Mutumin da yazo na biyu shine shugaban kamfanin Amazon kuma mamallakinsa, Jeff Bezoz, wanda yake da arzikin dala biliyan $194bn.

Attajiri na uku mafi kuɗi a duniya shine Bernard Arnault, ɗan kasar Faransa wanda ya mallaki dala biliyan $174bn.

A baya dai shugaban kamfanin Microsoft, Bill Gates, shike rike da matsayi na uku amma yanzun an kere shi.

Punch ta ruwaito cewa ana ganin dai kuɗin Bill Gates ya ragu ne sanadiyyar rabuwar da ya yi da matarsa Melinda Gates a yan kwanakin baya.

Mamallakin shafin sada zumunta wato Facebook, Mark Zuckerberg, shine na biyar a jerin masu kuɗin duniya inda yake da dukiyar da takai dala biliyan $135bn.

A wani labarin kuma Fitaccen ɗan kwallon kafa na duniya, Lionel Messi, ya amince da kulla yarjejeniya a kungiyar PSG ta kasar Faransa

Ɗan wasan wanda ya bar tsohuwar kungiyarsa Barcelona a makon da ya gabata ya samu ta yi guda biyu amma ya zaɓi tafiya PSG ta kasar Faransa.

Kara karanta wannan

Kyari-Hushpuppi: An zargi Dino Melaye da karbar na shi rabon $31m, ya karyata

Messi wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan kwallo na duniya Ballon d'Or sau shida zai kwashi kuɗi kimanin £25m duk shekara bayan cire haraji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel