Daga ayyana gina jami'ar Muslunci a Katsina, Okorocha ya rasa sarautarsa a kudu

Daga ayyana gina jami'ar Muslunci a Katsina, Okorocha ya rasa sarautarsa a kudu

  • Rahotanni sun bayyana cewa, an karbe nadin saarautar da aka yiwa Rochas Okorocha a jihar Ogun
  • Wannan ya faru ne jim kadan bayan da Rochas ya ayyana cewa, zai gina jami'ar musulunci a Katsina
  • Sai dai, sanarwar ba ta ambaci alakar gina jami'ar da karbe sarautarsa ba, ta kuma bukaci ya ci gaba da aikin taimako

Ogun - Oba Ebenezer Akinyemi, Eselu na Iselu ya soke nadin tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, a matsayin Otunba Asoludero na Iselu a karamar hukumar Yewa ta Arewa a jihar Ogun.

Nigerian Tribune ta rahoto cewa basaraken gargajiyar ya bayyana haka a cikin wata wasika da ya aike wa sanatan, duk da cewa, bai bayyana dalilin soke nadin ba.

A cewar Oba Akinyemi, soke nadin da soke bikin nadin ba don kiyayya ga Okorocha ba ne, sai don son zaman lafiya da jituwa, jaridar Punch ta kara da cewa.

Kara karanta wannan

Kungiyar dalibai ta NANS ta kai kukan ta ga Sheikh Gumi da Buhari kan sace dalibai

Yayin da yake rokon sanatan da ya yarda da sokewar a matsayin kaddara daga Allah, sarkin gargajiyar ya kuma shawarci Okorocha da ya ci gaba da taimaka wa mabukata sannan kuma kada ya yi kasa a gwiwa wajen taimakawa wajen bunkasa yankin Iselu da Najeriya baki daya.

Bikin nadin Okorocha a matsayin Otunba Asoludero na Iselu bisa wasikar karbarsa ta nuna 19 ga Satumba.

Daga ayyana gina jami'ar Muslunci a Katsina, Okorocha ya rasa sarautarsa a kudu
Sanata Rochas Okorocha | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sanata Rochas Okorocha zai gina Jami’ar musulunci a Mahaifar Shugaba Buhari a Katsina

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi alkawarin gina jami’ar addinin musulunci a mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Premium Times ta ce Sanata Rochas Okorocha ya bayyana cewa gidauniyar nan ta sa, Rochas Okorocha Foundation, za ta yi wannan babban aikin.

Jigo kuma Sanatan na jam’iyyar APC zai kafa wannan jami’a ne a garin Daura, Arewacin jihar Katsina.

Kotu ta ce a karbe kadarori fiye da 500 da tsohon Gwamnan APC ya mallaka lokacin ya na ofis

Kara karanta wannan

Sam ba a yi wa Abba Kyari adalci ba: 'Yan Arewa sun koka kan kwace mukamin Kyari

A wani labarin, Wani babban kotu da ke zama a garin Owerri, jihar Imo, ya bada umarni a karbe wasu kadarori fiye da 500 na tsohon Gwamna, Rochas Okorocha.

Kotu ta bukaci a karbe wadannan dukiyoyi da tsohon gwamnan ya samu a lokacin da yake ofis.

Jaridar The Nation ta ce an zartar da wannan hukunci ne a shari’ar da ake yi tsakanin babban lauyan gwamnatin jihar Imo da su Nkechi Rochas Okorocha.

Misis Nkechi Rochas Okorocha ta na cikin shugabannin gidauniyar tsohon gwamnan na Rochas Foundation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel