Kotu ta ce a karbe kadarori fiye da 500 da tsohon Gwamnan APC ya mallaka lokacin ya na ofis
- Babban kotun jiha ta bada hukunci a shari’ar Rochas Okorocha da Gwamnatin Imo
- Alkali mai shari’a, Fred Njemanze yace lauyoyin Okorocha sun gaza kare shi a kotu
- Tsohon Gwamnan zai rasa dukiyoyin da ya tara a yayin da yake kujerar gwamnati
Imo - Wani babban kotu da ke zama a garin Owerri, jihar Imo, ya bada umarni a karbe wasu kadarori fiye da 500 na tsohon Gwamna, Rochas Okorocha.
Kotu ta bukaci a karbe wadannan dukiyoyi da tsohon gwamnan ya samu a lokacin da yake ofis.
Jaridar The Nation ta ce an zartar da wannan hukunci ne a shari’ar da ake yi tsakanin babban lauyan gwamnatin jihar Imo da su Nkechi Rochas Okorocha.
Misis Nkechi Rochas Okorocha ta na cikin shugabannin gidauniyar tsohon gwamnan na Rochas Foundation.
Shari'ar da aka yi
A wannan shari’a mai lamba HOW/M1191/2021, Alkali Fred Njemanze ya bukaci gwamnatin Imo ta karbe kadarorin na Rochas Anayo Okorocha har abada.
Independent ta ce daga cikin kadarorin Sanata Rochas Anayo Okorocha da na iyalan na sa da za a raba su da su akwai katafaren otel da wata jami'a a Ogboko.
Alkali mai shari’a, Fred Njemanze, ya ce Lauyoyin Rochas Okorocha ba su iya gamsar da kotu da hujjoji a kan abin da zai hana a karbe wadannan dukiyoyi ba.
Har ila yau Alkalin ya kara da cewa lauyoyin da su ka tsaya wa tsohon gwamnan ba su yi abin da ya kamata ba, ya ce sun buge ne da hargowa da soki-burutsu.
Lauyoyin Okorocha sun soki hukuncin da aka yi
Babban lauyan da ya kare Sanatan da iyalinsa a kotun, Oba Maduabuchi ya yi tir da hukuncin da Mai shari’a Fred Njemanze ya yi, ya ce ba ayi masu adalci ba.
Maduabuchi yake cewa ya yi mamaki da ya samu labarin cewa har Alkali ya zartar da hukunci bayan an yarda sai a yau (ranar Talata) ne kotu za ta zauna.
Kadarorin da aka karbe a hannun iyalin tsohon Gwamna
Sahara Reporters ta ce kadarorin su ne:
- Jami'ar Eastern Palm, Ogboko
- Otel din Royal Spring Palm Hotels and Apartments
- Rukunin gidajen IBC da aka damka wa makarantar Rochas Foundation College
- Rukunin gidajen Alkalai da ke titin Orli
- Ginin gwamnati da Nneoma Nkechi Okorocha ta gina shaguna
- Fuloti mai lamba P5, Naze Residential Layout a hanyar Aba da Nkechi Okorocha ta gina shaguna
- Da sauransu.
Asali: Legit.ng