Ya dasa sabon zargi: Abba Kyari ya goge wallafar da yayi a shafinsa inda yayi bayanin alakarsa da Huspuppi
- Dakataccen DCP na 'yan sanda, Abba Kyari ya goge wani rubutu da ya wallafa a Facebook inda ya bayyana alakarsa da Hushpuppi
- Bincike ya nuna cewa Kyari ya yi wasu gyare-gyare da dama a cikin wallafar nasa kafin daga bisani ya goge rubutun gaba daya
- An tattaro cewa wannan abu da yayi ya haifar da karin zargi a zukatan wasu mutane da ke bibiyar lamarin
Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari, ya goge wani rubutu da ya wallafa a Facebook inda ya bayyana alakarsa da wanda ake zargi da damfara ta intanet, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.
Hushpuppi ya ambaci Mista Kyari, a matsayin wanda ya karbi wani bangare na kudaden zamba wanda ake tuhumarsa akai a kasar Amurka.
Hushpuppi, wanda ya amince da aikata laifin zambar, ya shaida wa masu gabatar da kara na Amurka cewa ya ba Mista Kyari wani bangare na kudaden da aka samu daga laifin.
Allah Zai Wanke Abba Kyari, Hassada Wasu Ƴan Sanda Ke Masa: Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin ‘Brekete Family’
Ya ce ya kuma sa Mista Kyari ya kamo daya daga cikin abokan aikinsa na Najeriya lokacin da suka samu sabani.
Mista Kyari ya je shafinsa na Facebook don wanke kansa tare da nuna cewa ba shi da laifi.
Abba Kyari ya ce bai karbi ko sisin kwabo daga wajen Hushpuppi ba, illa ya ce ya ga wasu kaya da huluna a shafinsa, sai yace yana so kuma aka hadashi da mai sayar da kayan kuma ya turawa mai kayan kudi N300k."
Ya yi gyare-gyare sannan ya goge wallafar daga shafinsa
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa binciken da ta yi a ranar Talata ya nuna cewa Kyari ya yi gyare-gyare da yawa a rubutun nasa kuma ya fitar da sashin da ya yi ikirarin cewa ya hada Hushpuppi da telansa.
Ya kuma gyara ikirarin da yayi na N300,000 sannan ya kara wani sashi inda ya ambaci N8m, jaridar Punch ta kuma ruwaito.
'Yan awanni kadan bayan gyara rubutun, sai aka cire shi gaba daya daga shafin nasa, lamarin da ya kara haifar da karin zargi.
'Yan Najeriya da yawa sun soki Mista Kyari sosai bayan kalamansa da yake mayar da martani.
FBI: A karshe Abba Kyari ya bayyana a gaban kwamitin bincike na 'yan sanda
A halin da ake ciki, mun kawo a baya cewa Abba Kyari ya gurfana a gaban kwamitin bincike na musamman kan tuhumarsa a badakalar Hushpuppi.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa har zuwa lokacin da aka dakatar da shi, Kyari shine shugaban dakarun IRT masu tattara bayanan sirri, kuma kwamitin da ke binciken sa yana karkashin Joseph Egbunike, mataimakin babban sufeton yan sanda mai kula da sashin binciken manyan laifuka na rundunar.
Asali: Legit.ng