Daga Karshe, Atiku Ya Magantu Kan Rikicin Dake Faruwa a Jam'iyyar PDP, Ya Fadi Mafita

Daga Karshe, Atiku Ya Magantu Kan Rikicin Dake Faruwa a Jam'iyyar PDP, Ya Fadi Mafita

  • Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, yace dole ne shugabannin PDP su haɗa kansu
  • Atiku yace bai kamata ana samun irin wannan hatsaniyar a dai-dai wannan lokacin ba kuma a cikin PDP
  • Hakanan Atiku ya musanta zargin cewa yana da hannu a kitsa rikicin dake karuwa

Abuja:- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga shugabannin PDP da su haɗa kansu domin cigaban jam'iyyar da kasa baki ɗaya.

Atiku ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da kakakinsa, Paul Ibe, ya fitar ranar Alhamis a Abuja yayin da yake martani kan sabon rikicin da ya kunno.

Punch ta rahoto Atiku yace PDP ba zata yarda a raba ta a dai-dai lokacin da yan Najeriya ke Allah-Allah su samu canjin gwamnati.

Atiku yace a matsayinta na jam'iyyar adawa ya kamata ta gaggauta nemo hanyar warware matsalar domin bai kamata a zuba wa jam'iyya mai mulki ido tana cin karenta babu babbaka.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Cike da tashin hankali, Secondus ya koka kan yunkurin 'kwace' PDP

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar
Daga Karshe, Atiku Ya Magantu Kan Rikicin Dake Faruwa a Jam'iyyar PDP, Ya Fadi Mafita Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Dagaske ne Atiku na cikin masu rura wutar rikicin?

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya musanta zargin da ake masa cewa yana da hannu a wajen rura wutar rikicin dake faruwa a PDP.

Atiku ya kara da cewa bada jimawa ba yana daga cikin waɗanda suka jagoranci sulhu a faɗin kasar nan kuma ya yi imanin ta wannan hanyar ne kaɗai komai zai dai-daita, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Wani sashin jawabin yace:

"Jam'iyyar PDP ta zarce bukatun mu na kai da kai, ya kamata mu kintsa kanmu kafin mu fara maganar muradin mu. Wajibi ne mu kula sosai domin kome muka yi jam'iyya mai mulki tana kallo."
"Ba zamu bari jam'iyya ɗaya ta cigaba da mulkin Najeriya ba domin hakan zai sa fatan mutane na samun canji a 2023 ya bi iska."

Menene babbar matsalar da hanyar magance ta?

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa karkashin PDP ɗin ya yi gargaɗin cewa rashin haɗin kai da amincewa juna zai taimakawa jam'iyya mai mulki fiye da PDP.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jiga-Jigan PDP Sun Shiga Taron Gaggawa Kan Wani Sabon Rikici da Ya Kunno

Ya kara da cewa mai son Najeriya ta cigaba da kasancewa a halin da take ciki ne kaɗai zai so rikicin PDP ya ɗore.

Atiku yace ya zama wajibi jiga-jigan PDP su jingine duk wani banbanci gefe guda su yi aiki tukuru domin goben jam'iyya.

A wani labarin kuma Abinda Muka Tattauna da Jagoran APC Bola Tinubu a Birnin Landan, Gwamna

Gwamna Sanwo-Olu ya shaidawa manema labarai a gidan gwamnati dake Ikeja, cewa yayin ziyararsa sun tattaunawa abubuwa da dama waɗanda suka shafi APC da Tinubu.

Gwamnan ya ƙara da cewa ya ɗauki hotuna da jigon APC ne saboda ya karyata jita-jitar dake yawo cewa an kwantar da shi a asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel