Da Duminsa: Yan Majalisa Sun Zabtare Kudaden da Tsaofaffin Gwamnoni Suke Karba Duk Wata

Da Duminsa: Yan Majalisa Sun Zabtare Kudaden da Tsaofaffin Gwamnoni Suke Karba Duk Wata

  • Majalisar dokokin jihar Lagos ta zabtare kuɗin fanshon tsofaffin gwamnonin jihar da kashi 50%
  • Majalisar ta kuma soke basu gidajen zama a babban birnin tarayya Abuja da kuma jihar Lagos
  • Hakazalika an rage yawan motocin da za'a basu da kuma lokacin canza musu motocin

Lagos:- Majalisar dokokin jihar Lagos, ta zabtare kuɗin fanshon tsofaffin gwamnonin jihar da kashi 50%, kamar yadda punch ta ruwaito.

A wata sanarwa da majalisar ta fitar ranar Alhamis, tace an ɗauki wannan matakin ne bayan amincewa da rahoton da wani kwamitinta ya gabatar.

Rahoton ya shawarci a zabtare kuɗin fanshon da tsofaffin gwamnoni suka karba duk wata da kashi 50%, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Yan majalisar dokokin Lagos sun zabtare albashin tsaffin gwamnoni
Da Duminsa: Yan Majalisa Sun Zabtare Kudaden da Tsaofaffin Gwamnoni Suke Karba Duk Wata Hoto: punchng.com
Asali: UGC

An soke basu gidaje a Abuja

Hakanan kwamitin ya soke baiwa tsofaffin gwamnonin gida a Abuja da kuma Lagos, yayin da za'a koma amfani da ɗokar jihar ta asali.

Wani bangaren jawabin yace:

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kallo Ya Koma Sama Yayin da Wani Gwamna Ya Dira Dakin Taron Dattijan PDP

"Mun ɗauki wannan matakin ne bayan amincewa da rahoton kwamitin kaddamarwa."
"Mun rage kuɗin fanshon tsofaffin gwamnoni da manyan jami'an gwamnati da kashi 50, kuma an soke basu gidaje a Abuja da Lagos."
"Sannan za'a rage yawan motocin da ake baiwa tsofaffin gwamnoni da kuma mataimakansu."

Motoci nawa za'a rinka ba su?

Kakakin majalisar dokoki ta jihar Lagos, Mudashiru Obasa, ya bada shawarar cewa kamata yayi a basu motoci biyu maimakon uku da kwamitin ya bada shawara.

Hakanan kuma ya kara da cewa kamata ya yi a rinka canza musu motocin duk bayan shekara huɗu maimakon uku kamar yadda rahoton yace.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Ganduje Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Yan Kungiyar IPOB da Yarbawa Dake Son Ballewa

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, yace kokarin ballewa daga ƙasa ba shine hanyar warware ƙalubalen da muke fama da shi ba.

Najeriya na fama da masu fafutukar ballewa daga cikinta daga kungiyar masu son kafa kasar Biyafara (IPOB) da kuma ta yarbawa "Jamhuriyar Odudua.'

Kara karanta wannan

Osinbajo su na kokarin fitar da APC daga tirka-tirkar shari’ar da za a iya shiga nan gaba

Asali: Legit.ng

Online view pixel