Yadda masu tattara shara suka dawowa da tsohuwa N10,287,000 da ta zuba a shara

Yadda masu tattara shara suka dawowa da tsohuwa N10,287,000 da ta zuba a shara

  • Labari mai ban al'ajabi na wasu ma'aikatan zubar da shara masu gaskiya daga kasar Amurka ya dauki hankali
  • An ruwaito yadda wasu dangi suka yi kuskuren zubar da makudan kudade cikin shara mallakar wata tsohuwa
  • Rahoton ya ce, tuni aka bi diddigi har aka gano motar da ta debi sharan sannan aka dawo wa da tsohuwar kudinta

Ohio, Amurka - Wasu dangi a kasar Amurka, Ohio, an ce sun zubar da tsabar kudi $25,000 (N10,287,000) cikin kuskure lokacin da suke taimaka wa kakarsu a aikin tsaftace gida.

Wannan ya faru ne a gundumar Lorain in ji rahoto. An ce dangin sun ci sa’a, wani kamfanin tattara shara ya yi nasarar lalubo shara sannan ya kwaso kudin bayan zubar da kunshin kudin. A cewar ABC News 5, tuni aka mika kudin ga tsohuwa mai kudin.

A cewar Ohio Insider, mai kula da ayyukan tattara sharan, Gary Capan ya ce tawagarsa ta taimaka wa dangin da ba a ambaci sunansu ba wajen gano kudin tsohuwar.

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

Dalolin Amurka | Hoto: economicconfidential.com
Yadda masu tattara shara suka dawowa da tsohuwa N10,287,000 da ta zuba a shara
Asali: UGC

Dangin sun tabbatar da gano makudan kudaden

Rahoto ya nakalto Capan yana tabbatar da cewa sun sami nasarar gano dangin da suka jefar da kudin kuma sun dawo musu da tsabar kudin.

Ya bayyana yadda lamarin ya faru da, cewa tawagarsa ta samu kiran gaggawa daga dangin don bin diddigin direban motar da ta kwashi sharan.

A cewarsa:

"Suna tsaftace gidan kakarsu ce kawai sai suka tattara komai na cikin wani firiji, sun zubar da duk wani dattin ciki, sun kwashe duk kayan daskarewan cikinsa suka saka a cikin jaka.
"Sannan ne sai kakar ta ce, 'Kai, akwai ambulaf dauke da $25,000 a ciki, kar ku tattara dashi.' "Idan an zubar da kudin a wurin zubar da shara, ba za a sake samun su ba."

Kamfanin tattara shara ya magantu kan lamarin

A cewar Ampgoo, dangin sun yi matukar sa’a a lokacin da masu tattara shara suka yi nasarar gano kudin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari wani kauye, sun yiwa mai gari yankan rago

Dan Schoewe ya ce:

"Ya dauki tsawon mintuna 10 kafin a gano kudin, Malam, kamar wasa, ana ciro shi, ana bude shi kuma sai ga kunshin dauke da kudin. Sun yi farin ciki sosai don an taimake su."

Abubuwan da ya kamata ku sani tsakanin kudin intanet na Najeriya da Bitcoin

A wani labarin, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da cewa zai kaddamar da tsarin gwajin kudin intanet da aka yiwa lakabi da eNaira zuwa 1 ga Oktoba, 2021, The Cable ta ruwaito.

Rakiya Mohammed, daraktar fasahar bayanai na CBN, ta bayyana hakan ne yayin wata ganawa ta kafar yanar gizo tare da masu ruwa da tsaki a ranar 22 ga Yuli.

Ta bayyana cewa babban bankin ya fara bincike kan kudin intanet na Babban Bankin (CBDC) tun cikin 2017.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.