Da Duminsa: Sojoji sun ceto daliban da aka sace a Kaduna daga 'yan bindiga
- Wasu daga cikin daliban da aka sace a wata makarantar Baptist sun kubuta daga hannun 'yan bindiga
- Wasu sojojin Najeriya ne suka samo su, kuma suka dauko su zuwa cikin gari domin sada su da iyayensu
- A halin yanzu, hukumomin tsaro basu tabbatar da faruwar lamarin ba, amma mazauna sun shaida hakan
Kaduna - An sake gano wasu dalibai uku da aka sace na makarantar sakandare ta Baptist Baptist dake jihar Kaduna.
Sojoji sun gano daliban uku (dukkansu maza) a babban dajin Kankumi da ke karamar hukumar Chikun inda masu garkuwa da mutanen suka yi watsi da su.
Duk da cewa har yanzu rundunar 'yan sanda ko hukumar makarantar ba su tabbatar da faruwar lamarin ba, amma mazauna yankin sun shaidawa gidan talabijin na Channels cewa daliban uku sun tsere daga hannun 'yan bindiga.
Bayan sace su daga makarantarsu a ranar 8 ga watan Yuli, an rahoto cewa wasu gungun 'yan bindiga sun sake sace su yayin da suke yawo a cikin daji.
An ce rukunin 'yan bindigan na biyu sun sake tattaunawa da iyalansu kuma sun karbi kudin fansa daga iyayen daliban uku, bayan nan suka jefar da su cikin daji kafin daga bisani sojoji suka same su.
Yanzu haka sojoji sun yi wa daliban bayani, kuma za su mika su ga hukumomin makarantar nan ba da jimawa ba.
Yadda aka tsinci gawar wani jami'in JTF a karkashin gada a Abuja
An gano gawar wani jami’in hadin gwiwa (JTF) a gadar Gwagwalada da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja a babban birnin kasar.
Daily Trust ta gano cewa gawar jami’in, wanda ke sanye da kaki, ya huje da harbin harsashi.
Matafiya sun gano gawar, wacce daga baya jami’an tsaro suka dauke ta, ranar Talata 3 ga watan Agusta, 2021.
Wani shaida, wanda aka bayyana sunansa da Gabriel, ya ce an gano gawar ne a gaban Otal din Brifina da ke Gwagalada.
Yadda 'yan sanda suka cafke wani da ake zargin yana karbar kudin fansa ta asusun banki
A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a Suleja, Jihar Neja, ta cafke daya daga cikin wadanda ake zargin mai satar mutane ne da ke karbar kudin fansa ta banki a Babban Birnin Tarayya (FCT).
Wannan kenan kamar yadda mai asusun bankin da mai garkuwa da mutanen ya yi amfani da shi, Babawi Abba, ya dauki lauya don ya kare kansa domin ya tabbatar da cewa ba shi da laifi a cikin lamarin.
Daily Trust ta ruwaito cewa mijin daya daga cikin wadanda aka sace, Saheed Adewuyi cewa, ya biya N500,000 a cikin wani asusun bankin Access mai lamba 1403762272 da suna Badawi Abba Enterprise.
Asali: Legit.ng