Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Kutsa Wurin Ibada Sun Hallaka Babban Malami Yana Tsaka da Addu'a
- Wasu yan bindiga sun kutsa cikin wata coci a Lagos, inda suka harbe fasto har lahira
- Rahotanni sun bayyana cewa sai da suka nunawa faston hotonshi domin ya tabbatar da shi suka zo kashewa
- Hukumar yan sanda tace ta kaddamar da bincike na musamman domin tana da wata karamar shaida
Lagos:- Wasu yan bindiga sun kutsa wurin ibadar kirista (Cocin RCCG) sun harbe Fasto Bolanle Ibrahim, har lahira a jihar Lagos.
Dailytrust ta ruwaito cewa an kashe Ibrahim ne akan mumbarin cocin dake Kauyen Maidan, karamar hukumar Ikosi Ketu, jihar Lagos.
Rahoto ya nuna cewa mamacin yana tsaka da addu'a ga wata mata yayin sadaukarwa ga 'ya'ya lokacin da maharan suka afka cikin cocin.
Yan bindigan sun yi kokarin tafiya da Fasto Ibrahim, amma wani babban fasto na gaba da shi ya dakatar da su da tambayar me suke bukata.
Me yan bindigan suka zo nema?
Yar uwar faston da aka kashe, Mrs. Justina Alebiosu, ta bayyana lamarin da wani shiryayyan kisan kai.
A jawabinta tace:
"Kafin su kashe shi sai da suka nuna masa hotonsa domin ya tabbatar shine suka zo dominsa. Mutuwarsa ta zo mana bagatatan kuma mun yi babban rashi."
"An haife mu a cikin addinin musulunci amma daga baya muka koma kiristanci, a tunani na ɗan uwa na yana da wata alakar kasuwanci da wani."
"An faɗa mun cewa yayin da maharan suka yi kokarin tafiya da shi yana tsaka da yiwa wata mata addu'ar sadaukarwa ga ƴaƴanta, sai ya nemi su kashe shi anan kuma suka aikata haka."
Ta kara da cewa maharan sun yi barazanar harbe duk wani dake cikin cocin idan ya yi kokarin hana su aiwatar da abinda ya kawo su.
A taimaka mana mu binne ɗan uwanmu
Mrs. Alebiosu ta yi kira ga kwamishinan yan sanda na jihar, Hakeem Odumosu, ya taimaka a basu gawar ɗan uwan su mata jana'iza.
Matar faston, Mrs. Kudirat Ibrahim, ta bayyana cewa da azumi a bakin mijinta a ranar da aka kashe shi, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Mrs. Ibrahim ta kuma musanta jita-jitar da wasu ke yaɗawa cewa mijinta ɗan kungiyar asiri ne kuma kisan shi na da alaƙa da haka.
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Lagos, CSP Muyiwa Adejobi, wanda ya tabbatar da lamarin, yace an kaddamar da bincike na musamman domin kamo waɗanda suka aikata kisan.
Yace: "A halin yanzun muna bincike a kan lamarin saboda muna da wata shaida game da kisan."
Yace kwamishinan yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, ya umarci wata tawagar kwamandoji su jagoranci binciken.
Ya kuma kara da cewa kwamishinan ya ɗauki matakai da dama domin magance ayyukan yan ƙungiyar asiri a yankin Mile 12 da Ketu.
A wani labarin kuma Wata Cuta Mai Saurin Yaduwa Ta Barke a Sokoto, Ta Hallaka Mutum 23 Wasu 260 Sun Kamu
Akalla mutum 23 sun mutu sanadiyyar barkewar wata cuta da ake kira 'gastroenteritis' amma an fi sanin ta da murar ciki a wasu ƙauyukan Sokoto.
Kwamishinan lafiya na jihar, Muhammed Iname, shine ya tabbatar da haka a taron manema labarai ranar Talata.
Asali: Legit.ng