Majalisar wakilai ta magantu kan karrama Abba Kyari da ta yi a matsayin gwarzo

Majalisar wakilai ta magantu kan karrama Abba Kyari da ta yi a matsayin gwarzo

  • Majalisar wakilai ta bayyana matsayinta kan zargin da ake wa Abba Kyari, ta ce har yanzu mutum ne na kwarai a idon ta
  • Wannan ya biyo bayan zargin da aka yi wa Abba Kyari ne da aikata karbar rashawa daga hannun wani dan damfara
  • Majalisar a baya ta karrama Abba Kyari bisa ayyukansa na kirki ga Najeriya da hukumar 'yan sanda

Majalisar wakilai ta ce Abba Kyari zai ci gaba da kasancewa mai mutunci a idon majalisa har sai an same shi da laifin tuhumar da hukumar bincike ta FBI da ke Amurka ta yi masa.

Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta dakatar da Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda bisa shawarar Sufeto Janar na 'yan sanda IGP, Usman Baba, har zuwa lokacin da hukumomin 'yan sandan Najeriya za su gudanar da bincike akansa.

Majalisar wakilai ta magantu kan karrama Abba Kyari da ta yi a matsayin gwarzo
Abba Kyari | Hoto: Abba Kyari
Asali: UGC

Majalisar wakilai ta karrama Abba Kyari a watan Yunin bana

A watan Yunin 2020, majalisar wakilai sun karrama Kyari haifaffen jihar Borno saboda kyakkyawan aikin da ya yi wa rundunar 'yan sandan Najeriya da ma Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

Gayyatar da karramawar ta biyo bayan bukatar da dan majalisar da ke wakiltar mazabar tarayya ta Chibok a jihar Borno, Ahmad Jaha, ya gabatar kwanaki biyu kafin zuwansa majalisar.

Lokacin da jaridar Punch ta tuntube shi don yin magana kan karramawar da aka yi wa Kyari, bayan da aka zargi dan sandan da aikata abin kunya, Benjamin Kalu, ya ce DCP har yanzu bai da laifi har sai an tabbatar da laifinsa.

Kalmomin sa:

“Matsayin dokar mu ita ce ba ka da laifi har sai an tabbatar da ka aikata laifi. Ba shine kadai lambar yabo da yake da ita ba. Ba za mu karbe lambar yabon mu ba; shi ake zargi a halin yanzu. 'Yan majalisa ba masu karya doka ba ne.
“Kundin tsarin mulki ya ce ba ka da laifi har sai an tabbatar da laifin ka. Amma idan a karshe, aka kama shi da laifi, to majalisar za ta sami dalilin sake duba matsayin ta. Amma a halin yanzu, har yanzu ana kan bincike.”

Kara karanta wannan

Babban lauya ya ce akwai bukatar mika Abba Kyari ga FBI, ya fadi dalili

Babban lauya ya ce akwai bukatar mika Abba Kyari ga FBI, ya fadi dalili

Shahararren lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan adam, Cif Femi Falana (SAN) ya yi kira ga Babban Lauyan Tarayya (AGF) kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, da ya aiwatar da bukatar Amurka ta mika mata Abba Kyari akan ka'ida.

Falana ya ce Kwamitin Bincike na Musamman da Babban Sufeto Janar ya kafa Babban Sufeto kan lamarin da ake dubawa ya kamata ya yi cikakken aiki.

Da yake magana yayin wata hira ta wayar tarho da gidan Talabijin na Afirka mai zaman kansa wanda jaridar Daily Sun ke sa ido, Falana ya bayyana cewa Kyari ya samu ne daga tsarin gwamnatin da ya gaza.

Ofishin Abubakar Malami ya magantu kan zargin da ake wa Abba Kyari

A wani labarin, Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, kuma ministan Shari'a Abubakar Malami, ta ce har yanzu ba ta karbi wata takarda a hukumance daga cibiyar binciken Amurka ta FBI ba da ke neman damar kame mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari.

Kara karanta wannan

Ofishin Abubakar Malami ya magantu kan zargin da ake wa Abba Kyari

Wannan ya fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga ministan, Umar Gwandu yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar Punch.

FBI ta zargi Abba Kyari da karbar cin hanci daga hannun Hushpuppi, wani dan damfara dake fuskantar zaman kotu a Amurka, bayan kame masa wani abokin harkallarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel