Bayan Hana Yan Najeriya Su Zabi PDP da APC, Farfesa Jega Zai Tsaya Takara a Zaben 2023
- Tsohon shugaban INEC, Farfesa Jega, ya bayyana cewa zai tsaya takara a babban zaɓen 2023 dake tafe
- Jega ya kara da cewa ya shiga jam'iyyar PRP ne domin ya bayad da ta shi gudummuwar a siyasance
- Babban malamin jami'ar ya yi kira ga yan Najeriya da kada su sake kuskuren zaɓar manyan jam'iyyu PDP da APC
Abuja - Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa ya shiga jam'iyyar PRP ne domin ya bada gudummuwarsa a siyasance.
Jega ya kara da cewa zai tsaya takara a zaɓen 2023 dake tafe amma ya zuwa yanzun bai yanke shawara a kan mukamin da zai tsaya takara ba.
Farfesa Jega ya faɗi haka ne a wata hira ta musamman da ya yi da sashen Hausa na BBC.
Kada ku zaɓi APC da PDP
Babban malamin jami'ar ya yi kira ga yan Najeriya kada su kuskura su sake zaɓen manyan jam'iyyu biyu APC da PDP a zaɓen 2023 dake tafe.
Tsohon shugaban hukumar INEC yace jam'iyyar APC da ta adawa PDP ba su da kwarewar cigaba da jagorancin ƙasar nan a yanzu.
A jawabinsa, Jega yace:
"Manyan jam'iyyun kasar nan biyu APC da PDP ba su cancanci ci gaba da jagorancin kasar ba, basu da kwarewar da ake bukata."
"Ina kira ga yan Najeriya (kasar da tafi yawan jama'a a Nahiyar Afirka) da kar su sake zaɓen su a babban zaben 2023 dake tafe"
APC da PDP sun maida martani
Sai dai a bangaren manyan jam'iyyun biyu sun maida martani a kan kalaman da Farfesa Jega ya yi akan su.
A cewar jam'iyyun sam abinda ya faɗa ba gaskiya bane, suka ce kawai irin ta siyasa.
A wani labarin kuma Shahararren Dan Kasuwa, Okunbo, Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Shugaba Buhari Ya Yi Jimami
Babban attajirin ɗan kasuwa kuma haifaffen jihar Edo, Capt. Idahosa Wells Okunbo, ya rigamu gidan gaskiya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Okunbo, wanda sirikin babban basaraken Wari ne, ya kwanta jinyar rashin lafiya a wani asibiti da ba'a bayyana ba a birnin Landan.
Asali: Legit.ng