Gwamnatin jihar Oyo ta bada hutu ranar Talata don murnar sabuwar shekarar Hijra 1433
1 - tsawon mintuna
Gwamnatun jihar Oyo, ta sanar da ranar Talata, 10 ga watan Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci - Hijrah 1443 AH.
Wannan na kunshe cikin jawabin da Sakataren gwamnatin jihar, Mrs Olubamiwo Adeosun, ta saki ranar Juma'a a Ibadan, babbar birnin jihar, rahoton Tribune.
Gwamnan ya yi kira ga Musulmai da masu bin sauran addinai suyi amfani da hutun domin addu'a ga cigaban jihar da Najeriya gaba daya.
Ranar farkon sabuwar shekarar Hijra zai kama ranar Litinin ko Talata dangane da ranar da aka ga wata.
Asali: Legit.ng