Bana Son Barin Barcelona, Messi Ya Fashe da Kuka Yayin Jawabin Bankwana

Bana Son Barin Barcelona, Messi Ya Fashe da Kuka Yayin Jawabin Bankwana

  • Shahararren ɗan wasan kwallon kafa, Lionel Messi, ya bayyana cewa ba'a son ransa zai bar Barcelona ba
  • Messi ya faɗi hakane yayin jawabin bankwana da ya yi ranar Lahadi a filin wasan Nou Camp
  • Ɗan wasan ya godewa dukkan abokan wasansa a Barcelona na yanzun da tsofaffi bisa irin gudummuwar da suka ba shi.

Barcelona, Spain - Tauraron ɗan kwallon kafa na duniya, Lionel Messi, ya bayyana cewa baya son barin Barcelona, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

A jawabin bankwana da ɗan wasan ya yi ranar Lahadi, ya godewa magoya bayan kungiyar Barcelona bisa nuna soyayyarsu garesa a kowane lokaci.

Messi ya yin da yake jawabin bankwana
Bana Son Barin Barcelona, Messi Ya Fashe da Kuka Yayin Jawabin Bankwana Hoto: Fabrizio Romano FB Fage
Asali: Facebook

A jawabinsa Messi yace:

"Barin Barcelona abune mai wahala a wurina bayan shafe shekaru masu yawa na kasance ina rayuwata a nan. Kwata-kwata ban shirya tafiya ba a yanzun"
"A yan kwanakin nan ina ta nazari kan abinda ya kamaya in faɗa muku, amma nakasa tunano komai. Wannan abu ne mai matukar wahala a wurina."

Kara karanta wannan

Ku kai yakin har zuwa mafakar makiya, COAS, Janar Yahaya ya umarci sojoji

"Na shafe tsawon rayuwata a anan, a zahirin gaskiya bana son barin Barcelona. Duk da abubuwa marasa daɗi da suka faru shekarar da ta gabata, na faɗi wasu abubuwa amma komai ya canza a wannan shekarar."
"Da ni da iyalaina mun yanke shawarar cigaba da zama a Barcelona wannan shekarar. Muna gida (Argentina) da tunanin zamu cigaba da zama anan."
"Amma duk lokacin da muka ɗauka a Barcelona muna wasan kwallon kafa abun mamaki ne ace mun barta. Sai dai ya zama wajibi na muku bankwana."
Lionel Messi
Bana Son Barin Barcelona, Messi Ya Fashe da Kuka Yayin Jawabin Bankwana Hoto: Fabrizio Romano FB Fage
Asali: Facebook

Watarana zan dawo Barcelona

Messi ya bayyana sha'awarsa na dawowa Barcelona nan gaba, inda ya kara da cewa bai yi tsammanin barinsa ƙungiyar a wannan lokacin ba.

Punch ta ruwaito Messi na cewa:

"Ina fatan zan dawo kuma na zama wani ɓangaren ƙungiyar Barcelona. Tun ina ɗan shekara 13 nake a nan amma bayan shekara 21 zan tafi da ni da matata da kuma 'ya'yan mu uku yan Kataloniya-Argentina."

Kara karanta wannan

Wata Amarya Ta Hallaka Angonta Kwanaki Kadan Bayan Sun Yi Auren Soyayya

"Ba zan iya faɗa muku komai ba amma muna fatan watarana zamu dawo nan saboda nan gidane a gare mu."

Messi ya godewa kowa da kowa

Lionel Messi ya mika sakon godiya ga abokan wasan sa na Barcelona da kuma tsofaffin abokan wasansa dama kowa dake ƙungiyar.

Ɗan wasan ya kara da cewa abubuwa masu daɗi da marasa daɗi sun faru yayin da yake kungiyar amma hakan kara masa karfin guiwa ya yi a kowane lokaci.

A wani labarin kuma Cuta Ta Barke a Jihar Katsina Ta Hallaka Akalla Mutum 60 Wasu 1,400 Sun Kamu

Akalla mutun 60 ne suka rasa rayuwarsu a faɗin kauyukan jihar Katsina bayan ɓarkewar cutar kwalara a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Yakubu Nuhu Danja, shine ya bayyana haka a wurin taron shekara-shekara na ƙungiyar likitoci (NMA).

Asali: Legit.ng

Online view pixel