Hotunan Osinbajo, Jonathan da jiga-jigan da suka halarci bikin diyar tsohon gwamna

Hotunan Osinbajo, Jonathan da jiga-jigan da suka halarci bikin diyar tsohon gwamna

  • An daura auren Adebola Williams, CEO din Red Africa da Kehinde Daniel, diyar tsohon gwanan jihar Ogun, Gbenga Daniel
  • Kasaitaccen binkin da zallar hamshakan mutane ne suka je ya faru ne a ranar Asabar a Otal din Federal Palace dake Vitoria Island a Legas
  • Cikin manyan ‘yan siyasar da suka hakarci bikin akwai Farfesa Yemi Osinbajo, Goodluck Jonathan, Kayode Fayemi da Rotimi Akeredolu

Victoria Island, Lagos - Lallai maganar hausawa gaskiya ce, daidai ruwa daidai kurji. An yi shagalin bikin Adebola Williams, CEO na Red Africa, wani kamfanin labarai, da Kehinde Daniel, diyar tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Deniel.

Shagalin da manyan mutane da dama suka halarta ya faru ne a ranar Asabar a Otal din Federal Palace dake Victoria Island a jihar Legas, TheCable ta wallafa.

Hotunan Osinbajo, Jonathan da jiga-jigan da suka halarci bikin diyar tsohon gwamna
Hotunan Osinbajo, Jonathan da jiga-jigan da suka halarci bikin diyar tsohon gwamna. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Bidirin da aka fara tun safe inda yara suka zagaya iyayensu suna sanyawa aurensu albarka sannan aka karasa bikin da misalin karfe 2pm bayan kowa ya ci ya kuma sha.

Kara karanta wannan

Wanda ya kashe mutum hudu a hadarin mota ba 'dan Umaru Yar'adua bane, dan Shehu Yar'adua ne

Wadanne baki ne suka halarci bikin?

Cikin kasaitattun mashahuran ‘yan siyasan da suka halarci bikin akwai mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da Rotimi Akeredolu, gwaman jihar Ondo.

Sannan akwai masu nishadantarwa da aka gayyata kamar Waje, Omawumi Megbele, Bovi, Timi Dakolo da Johnny Drille.

Adebola dan kasuwa ne dake harkar labari sannan Kehinde tana aiki ne da KPMG, wani kamfanine dake harkar kudi, TheCable ta ruwaito.

Hotunan Osinbajo, Jonathan da jiga-jigan da suka halarci bikin diyar tsohon gwamna
Hotunan Osinbajo, Jonathan da jiga-jigan da suka halarci bikin diyar tsohon gwamna. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Toshe bakin kafofin yada labarai ba zai yuwu ba, IBB yace

Tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce duk wani kokarin toshe bakin jama’a ba zai tabbata ba. Wannan mulkin yayi kokarin tsuke bakin jama’a tuntuni, duk da dai gwamnati ta dade tana musa wannan zargin.

Amma a wata tattaunawa da ARISE TV tayi IBB a gidansa dake hilltop a Minna, jihar Neja a ranar Juma’a, ya ce ‘yan Najeriya ba zasu taba barin hakan ya yuwi ba don zasu jajirce kwarai.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen dake faruwa a Plateau ya saba dokokin Allah, Malaman addinai sun yi tsokaci

Kokarin rufe bakin jama’a ba zai taba yuwuwa ba. Jama’a ba zasu taba barin hakan ya tabbata ba. Shirme ne kace zaka rufe bakin jama’a saboda kafafen sada zumunta ita ce kadai hanyar da jama’a suke da ita ta bayyana damuwarsu don haka abar su su yi yadda sukeso, a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel