Toshe bakin kafofin yada labarai ba zai yuwu ba, IBB yace

Toshe bakin kafofin yada labarai ba zai yuwu ba, IBB yace

  • Tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce duk kokarin rufe bakin jama’a ta kafar sada zumunta ba zai tabbata ba
  • Dama an dade ana zargin wannan mulkin sun yi iyakar kokarin ganin sun toshe bakin jama’a, duk da dai gwamnati ta dade tana musa wannan zargin
  • A wata tattaunawa da aka yi da IBB a ranar Juma’a a Minna, babban birnin jihar Neja, ya ce ‘yan Najeriya ba zasu taba barin hakan ya faru ba

Minna, Niger - Tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce duk wani kokarin toshe bakin jama’a ba zai tabbata ba.

Wannan mulkin yayi kokarin tsuke bakin jama’a tuntuni, duk da dai gwamnati ta dade tana musa wannan zargin.

Amma a wata tattaunawa da ARISE TV tayi IBB a gidansa dake hilltop a Minna, jihar Neja a ranar Juma’a, ya ce ‘yan Najeriya ba zasu taba barin hakan ya yuwi ba don zasu jajirce kwarai.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ku daina take umarnin kotu, tsohon shugaban kasa a mulkin soja ya gargadi DSS

Toshe bakin kafofin yada labarai ba zai yuwu ba, IBB yace
Toshe bakin kafofin yada labarai ba zai yuwu ba, IBB yace. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
Kokarin rufe bakin jama’a ba zai taba yuwuwa ba. Jama’a ba zasu taba barin hakan ya tabbata ba. Shirme ne kace zaka rufe bakin jama’a saboda kafafen sada zumunta ita ce kadai hanyar da jama’a suke da ita ta bayyana damuwarsu don haka abar su su yi yadda sukeso, a cewarsa.

IBB ya jinjinawa kokarin 'yan Najeriya

Ya nuna jin dadinsu akan jajircewar ‘yan Najeriyata yadda suka ki bari shugabanninsu su rufe musu bakunansu.

Tsohon shugaban kasar ya ce ‘yan Najeriya ba zasu taba tsayawa a wuri daya ba, jajircewar ‘yan Najeriya ne zai bunkasa kasar ta dawo hayyacinta.

'Yan Najeriya ba zasu bari su zama ‘yan jam’iyya daya ba. Za suyi magana, su yi nuni sannan su yi duk abinda sukeso ba tare da wani ya hanasu ba.

Mene ne babbar matsalar Najeriya?

IBB ya bayyana babbar matsalar Najeriya a matsayin zaluncin masu mulki amma su yi ta cewa rashin tsaro ne.

Kara karanta wannan

Bidiyon fusataccen dan Najeriya yana tallar ƙodarsa, yana tafe kan titi yana shela

Akwai rashin jituwa tsakanin shugabanni da mabiyansu. Ya kamata shugabanni su fahimci Najeriya da ‘yan Najeriya sannan yakamata su dinga yin abubuwa don cigaban jama’a.

Sannan ya kara baiwa ‘yan Najeriya kwarin guiwa da cewa har yanzu Najeriya bata gama lalacewa ba. Shugabanni zasu iya farfado da ita.

IBB: Dole ne shugaban kasa na gaba ya kasance masanin tattalin arziki

Tsohon shugaban kasan mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida wanda ake kira da IBB, ya ce ya kamata shugaban kasan Najeriya na gaba ya kasance mai fahimta a fannin tattalin arziki.

A yayin tattaunawa da Arise TV a ranar Juma'a, ya ce ya ga wasu mutanen dake da wannan nagartan kuma ya dace a ce sune suka samu shugabanci.

Idan muka samu shugaban mai nagarta dake alaka da mutane kuma yana kokari wurin magana da jama'a ba wai mai magana kan jama'a ba, tabbas komai zai daidaita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel