Kashe-kashen dake faruwa a Plateau ya saba dokokin Allah, Malaman addinai sun yi tsokaci
- Rikici a Pleteau kwanakin baya ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiya
- Gwamnatin Plateau ta ce an kwantan da kuran yanzu bayan kwanaki hudu
- Malaman addinai na jihar sun yi Allah-wadai da wannan kashe-kashe
Majalisar Malaman addinai a jihar Plateau ta yi Alla-wadai da kashe-kashe da asarar gonaki, gidaje da sauran dukiyoyi dake faruwa a wasu sassan jihar kwanakin nan.
Majalisar a jawabin da ta saki ranar Juma'a a Jos kuma shugabanninta Pandang Yamsat da Muhammadu Haruna, suka rattafa hannu, sunce wannan kashe-kashe ya saba dokokin Allah, rahoton DN.
Yamset Pandang shine tsohon shugaban cocin COCIN, yayinda Mohammadu Haruna shine Sarkin Wase kuma shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam, JNI, a jihar.
A cewar majalisar, wannan abu dake faruwa ya sabawa koyarwan addinin Musulunci da na Kirista.
Jawabinsu yace:
"Majalisar IRC wacce ta kunshi shugabannin Kirista da Musulunci a jihar Plateau sun yi Alla-wadai da bayyana fushinsu kan kashe-kashe, kone-konen gidaje da gonaki dake faruwa a Bassa, Riyon da Barkin Ladi."
"Wannan kashe-kashe gaba daya sun sabawa dokokin addinin Musulunci da Kirista; sun sabawa dokokin Allah kuma rashin tausayi ne. Kuma hakan na da hadari ga rayuka, abinci da tattalin arzikin jihar da kasar ga baki daya."
"A matsayinmu na Malaman addini, muna kira ga dukkan wadanda ke da hannu cikin wannan abu su sauya tunani kuma su tattauna da juna kamar da littafai addinai suka koyar."
Majalisar ta yi kira da gwamnati da jami'an tsaro su tsaurara matakan tsaro domin kawo karshen matsalar a jihar.
Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutane
Wasu yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun kai hari wasu kauyuka a ƙaramar hukumar Bassa, jihar Filato, kamar yadda punch ta ruwaito.
Yayin harin yan bindigan sun hallaka mutum huɗu tare da ƙona gidajen mutane da dama, kamar yadda Thisday ta ruwaito.
Rahotanni sun bayyana cewa harin, wanda ya bar mutane da dama cikin raunuka, ya faru ne lokacin mutane na bacci ranar Asabar da daddare.
Asali: Legit.ng