Ikon Allah: Hotunan kifi mai hakoran dan Adam da masunci ya kama sun bada mamaki

Ikon Allah: Hotunan kifi mai hakoran dan Adam da masunci ya kama sun bada mamaki

  • Wani kifi mai baki cike da hakora irin na dan Adam ya zama abun zance tun bayan bayyanarsa a Amurka
  • Masunci ne ya kama kifin a wani wurin kamun kifi dake arewacin Carolina, lamarin da ya baiwa jama'a mamaki
  • Kifin mai baki cike da turamen hakora tare da fikoki biyu an gano sunan shi sheepshead fish bayan Martin ya kama shi

A kasar Amurka, an kama wani irin kifi mai hakora tamkar na mutum, lamarin da ya firgita ma'abota zuwa teku shakatawa.

An kama wannan halittar ne a wani fitaccen wurin kamun kifi dake arewacin Carolina, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Tuni dai hotunan kifin suka bazu inda daga bisani aka gano cewa sunansa kifi mai kan tinkiya, wato sheepshead fish da turanci.

Ikon Allah: Hotunan kifi mai hakoran dan Adam da masunci ya kama sun bada mamaki
Ikon Allah: Hotunan kifi mai hakoran dan Adam da masunci ya kama sun bada mamaki. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Wani masunci mai suna Nathan Martin ne ya kama kifin mai bada al'ajabi kuma tuni hotunansa suka karade kafar sada zumunta ta Facebook.

Masuncin yace tuntuni yake da burin kama irin wannan kifin amma ya matukar shan mamaki bayan da yayi ido da ido da wannan kifi mai hakora cike da baki.

Kara karanta wannan

IBB: Dole ne shugaban kasa na gaba ya kasance masanin tattalin arziki

Artabu ne mai dadi idan kana artabu da halittun ruwa. Gaskiya nayi babban kamu kuma babu shakka zai yi dadi, ya sanar da McClatchy News.

Wannan irin kifin ya mallaki baki cike da turamen hakora tare da fikoki guda biyu, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Jama'a sun dinga ganin wannan kifi a matsayin wata sabuwar halitta.

Ikon Allah: Hotunan kifi mai hakoran dan Adam da masunci ya kama sun bada mamaki
Ikon Allah: Hotunan kifi mai hakoran dan Adam da masunci ya kama sun bada mamaki. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

IBB ya bayyana mummunan lamarin da zai auku da ba a soke zaben 12 ga watan Yuni ba

Tsohon shugaban kasan mulki soja, Ibrahim Babangida ya kara yin magana kan soke zaben 12 ga watan Yunin 1993 inda yace babu shakka mummunan juyin mulki za a tafka a kasar nan da ba a soke shi ba.

Zaben an yi shi ne tsakanin Bashir Tofa na jam'iyyar National Republican Convention (NRC) da MKO Abiola na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Duk da Abiola ne ya ci zaben kamar yadda sakamako ya nuna, an soke zaben tun kafin jami'ai su bada sanarwan wanda yayi nasara. Wannan al'amari kuwa ya janyo abubuwa da yawa saboda wasu jama'a sun fita titi zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel