Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari wani kauye, sun yiwa mai gari yankan rago

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari wani kauye, sun yiwa mai gari yankan rago

  • Rahotanni sun bayyana cewa, wasu 'yan bindiga sun kai hari wani yankin jihar Imo, sun hallaka mai gari
  • Hakazalika sun yi kaca-kaca da shagunan mutane yayin da babu wanda ya kawo dauki ga jama'ar yankin
  • Rahoton ya kuma bayyana yadda mutanen yankin suka shiga damuwa, suna kira ga taimakon gwamnati

Jihar Imo - Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari Okporo da makwabtanta a karamar hukumar Orlu ta jihar Imo.

Vanguard ta ruwaito cewa harin wanda aka fara a daren Lahadi, 1 ga watan Agusta ya ci gaba har zuwa safiyar Litinin, 2 ga watan Agusta.

Jaridar ta bayyana cewa har yanzu ba a san dalilin kai harin ba, inda ta kara da cewa mazauna garin sun danganta hakan da wasu gungun miyagu masu aikata miyagun laifuka da kuma wasu matsafa wadanda ke yin barna cikin dare.

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari wani kauye, sun fasa shaguna, sun yanka mai gari
'Yan bindiga | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

An kashe shugaban yankin

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun yi kakkausan martani kan kotun Amurka kan batun Abba Kyari

Sahara Reporters ta bayyana cewa maharan sun kashe wani shugaban yankin wanda ba a bayyana sunan sa ba.

Mazauna sun shiga tashin hankali

Jaridar Vanguard ta ambato wani mazaunin garin yana cewa tashin hankalin "ya yi zafi" saboda mutane ba su yi barci a daren da aka kai harin.

Majiyar ta ce:

"Wadannan masu aikata laifuka suna tafiya cikin walwala cikin dare kuma suna kashewa da lalata komai."

Mazaunin ya yi kira ga gwamnati da ta tura jami’an tsaro zuwa yankunan da ake rikici don kawo karshen hare-haren.

Yadda 'yan sanda suka cafke wani da ake zargin yana karbar kudin fansa ta asusun banki

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a Suleja, Jihar Neja, ta cafke daya daga cikin wadanda ake zargin mai satar mutane ne da ke karbar kudin fansa ta banki a Babban Birnin Tarayya (FCT).

Wannan kenan kamar yadda mai asusun bankin da mai garkuwa da mutanen ya yi amfani da shi, Babawi Abba, ya dauki lauya don ya kare kansa domin ya tabbatar da cewa ba shi da laifi a cikin lamarin.

Kara karanta wannan

Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano

Daily Trust ta ruwaito cewa mijin daya daga cikin wadanda aka sace, Saheed Adewuyi cewa, ya biya N500,000 a cikin wani asusun bankin Access mai lamba 1403762272 da suna Badawi Abba Enterprise.

Asali: Legit.ng

Online view pixel