A karshe IBB ya bayyana yadda aka yi masa lakabi da ‘mugun gwani’ da Maradona

A karshe IBB ya bayyana yadda aka yi masa lakabi da ‘mugun gwani’ da Maradona

  • Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), tsohon shugaban kasa, ya yi karin haske kan yadda ya samu laƙabi na mugun gwani da Maradona
  • Tsohon shugaban kasar na mulkin soja a ranar Juma’a, 6 ga watan Agusta, a wata hira da gidan talabijin na Arise yace kafafen yada labarai ne suka samar da sunayen
  • A cewarsa, an kira shi Maradona ne saboda dabarun siyasa

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya bayyana yadda aka yi masa lakabi da “evil genius” wato "mugun gwani" da "Maradona".

Babangida, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da Arise TV a wata hira da jaridar The Nation ta sa ido a ranar Juma’a, 6 ga watan Agusta.

A karshe IBB ya bayyana yadda aka yi masa lakabi da ‘mugun gwani’ da Maradona
IBB ya ce an lakaba masa Maradona ne saboda dabarun siyasa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya bayyana cewa kafafen yada labarai ne suka kakaba masa wannan sunan saboda "ƙaƙƙarfan salon siyasarsa".

Babaginda ya ce:

"Wannan abu ne mai kyau game da kafofin watsa labarai na Najeriya da mutanen Najeriya, dole ne ka hange su.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta

"Idan ka hange su to sai ka zauna lafiya da su. Suna kirana da 'mugun gwani', ina mamakin hakan. Ba za ka iya kasancewa mugu ba sannan ka zama gwani.”
"Ma'anar Maradona da na samu daga kafafen yada labarai shine saboda dabarun siyasa. Wannan shine yadda kafofin watsa labarai suka bayyana shi.”

Rashawa tayi katutu a gwamnatinka fiye da lokacin mulkina, IBB ga Buhari

A gefe guda, tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce yayi yaki da rashawa fiye da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban kasan Najeriya ya sanar da hakan ne yayin da tattauna da Arise TV a ranar Juma'a.

Ya ce mutanen da suka yi aiki a kasan shi waliyyai ne idan aka dangantasu da wadanda a halin yanzu suke mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel