Yanzu-yanzu: Ku daina take umarnin kotu, tsohon shugaban kasa a mulkin soja ya gargadi DSS
- Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida ya roki hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta daina take umarnin kotu
- IBB ya fadi haka ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na ARISE ranar Juma'a
- Babangida ya ce dole hukumar wacce aka kirkira a karkashinsa ta daina bijirewa umarnin kotu
Minna, jihar Neja - Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya roki hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta daina bijirewa umarnin kotu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa dattijon ya fadi haka ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na ARISE a ranar Juma'a, 6 ga watan Agusta
Babaginda ya ce dole hukumar wacce aka kirkira a karkashinsa ta daina sabawa umarnin kotu.
IBB ya zama shugaban kasa tsakanin 1985 zuwa 1993. An haife shi a jihar Neja, ya sami horon soji a Najeriya, Indiya, Burtaniya, da Amurka.
Ya rike mukamai kuma an san shi da ƙarfin gwiwa, kasancewar shi ma ya taka muhimmiyar rawa wajen murƙushe wani yunƙurin juyin mulki a 1976, lokacin da ya shiga gidan rediyon da ke hannun 'yan tawaye ba tare da makamai ba.
Hukumar DSS ta karyata zarginta da ake na tsare mutane ba bisa ka'ida ba
A gefe guda, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta zargin cewa ta tsare daruruwan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba bisa umurnin wasu manyan mutanen Najeriya.
Kamar yadda aka ruwaito, hukumar ta musanta hakan ne lokacin da take mayar da martani kan wani rubutun ra'ayi da wata jarida ta buga inda aka yi zargin.
Mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta, ya bayyana zargin a matsayin rashin fahimta da tunzura mutane, ya kuma bukaci mai maganar ya janye ikirarin.
Asali: Legit.ng