Ana batun karbar cin hancin Abba Kyari, magajin shi zai karbi kyautar $10,000
- Wani masanin fasahar sadarwa ya bayyana aniyar gwangwaje sabon shugaban tawagar IRT da kyauta
- Ya bayyana karara cewa, zai ba jami'in kyautar dala dubu 10 a madadin ilahirin matasa 'yan Najeriya
- Ya kuma yaba tare da nuna kwazon jami'in da kuma bayyana fatan 'yan Najeriya a kansa wajen gudanar da aiki
Aloy Chife, wani masanin fasahar sadarwa, ya yi wa Tunji Disu alkawarin $10,000 bisa nadinsa a matsayin shugaban tawagar 'yan sanda ta IRT.
Idan baku manta ba, Usman Alkali Baba, babban sufeton 'yan sanda (IGP), ya nada Disu a matsayin shugaban tawagar IRT bayan dakatar da Abba Kyari, wanda aka fi sani da gwarzon jami'in dan sandan Najeriya.
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta dakatar da Kyari bisa shawarar IGP kan zargin alakarsa da Ramon Abbas, dan damfara da aka fi sani da Hushpuppi.
Cikin farin ciki da nadin Disu, Chife ya bayyana jin dadinsa a kafar sada zumunta tare da nuna yabonsa da taya jami'in murna, in ji The Cable.
Ya bayyana Disu a matsayin "hasken fata" bayan haka ya yi masa alkawarin ba shi kyautar kudi a madadin 'yan Najeriya da "fatansu samun kwararrun 'yan sanda".
Chife ya taba fadi a wani sakon da ya wallafa a watan Janairu cewa Disu shine mutumin da ya fi cancanta ya zama IGP.
Bayan taya Disu murna, Chife ya ce:
“Zan ba ka $10k a madadin matasan Najeriya da suka dade suna fama a matsayin wata alama ta soyayya da ba da fata ga kwararrun 'yan sanda.
“Babu makoma ga Najeriya sai dai idan ta yi alfahari da samun kwararrun 'yan sanda.
“Kasashe masu nagarta suna ginuwa ne daga wasu zababbun mutane. Kuma kai, Mista Disu kana da alkawari tare da kaddara.
"Kuma dukkan mu muna matukar dakon nasarar ka."
Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya
A yayin da aka dakatar da shugaban rundunar IRT, Abba Kyari, Sufeto-Janar na 'yan sanda (IGP) Alkali Baba Usman ya gargadi dukkan jami'an da kada su kuskura su zubar da mutuncinsu a idon jama'a.
Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Usman, ya yi wannan gargadin ne yayin kaddamar da ayyukan miliyoyin nairori da Olusoji Akinbayo, kwamandan runduna ta “B”, Apapa ya yi.
Shugaban 'yan sandan wanda ya samu wakilcin Johnson Kokumo, Mataimakin Sufeto Janar na 'yan sanda (AIG) a sashen runduna ta 2 da ke jihar Legas, ya bayyana hakan ne a karshen mako.
Ya ce da zarar jami'i ya rasa goyon bayan jama'a to bai da wani dalilin da zai sadaukar da mutuncin ofishin sa.
FBI ba ta da ikon kame Abba Kyari, babban lauya Mike Ozekhome ya fadi dalili
A wani labarin, Babban Lauyan Najeriya, Mike Ozekhome (SAN), ya ce tilas Amurka ta gabatar da bukatar neman a mika mata mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, DCP Abba Kyari ta hanyar da ta dace.
Cibiyar Binciken Manyan Laifuka ta FBI ne ta zargi Kyari a wata tuhumar zamba da Ramon Abbas wanda kuma ake kira Hushpuppi ke fuskanta a Amurka.
Tuhumar Kyari ta biyo bayan umurnin kama shi daga wata kotun Amurka a gundumar tsakiyar California.
Asali: Legit.ng