Alkali ya yankewa Mutumin da ya zagi Buhari, Boss Mustapha hukuncin daurin shekara 2

Alkali ya yankewa Mutumin da ya zagi Buhari, Boss Mustapha hukuncin daurin shekara 2

  • DSS ta gabatar da Ikamu Hamidu Kato a wani karamin kotu da ke zama a Yola
  • Lauyoyi sun tabbatarwa Alkali cewa Ikamu Hamidu Kato ya zagi manyan kasa
  • Ikamu Kato ya amsa laifinsa, amma duk da hakan Alkali ya tura shi gidan yari

Adamawa - Hausawa sun ce baki shi yake yanka wuya. Hakan ya tabbata yayin da aka yanke wa wani ‘dan adawa da ya zagi shugabanni dauri a gidan maza.

A ranar Litinin, 2 ga watan Yuli, 2021, jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Alkali ya zartar da hukuncin daurin shekaru biyu a kan Ikamu Hamidu Kato.

Kotu ta yanke wa Mista Ikamu Hamidu Kato wannan hukunci ne saboda laifin zagin Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari da SGF, Boss Mustapha.

Wata kotun majistare da ke garin Yola, jihar Adamawa ta samu shugaban matasan PDP da aka dakatar, Ikamu Kato, da laifin zagin shugabannin Najeriya.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Yadda Gwamna Buni da Minista su ka sabawa umarnin Mataimakin Shugaban kasa

Alkalin da ya saurari wannan kara, Dimas Elishama, ya lafta wa Ikamu Kato tarar kudi N25, 000 baya ga zaman gidan gyaran hali da zai yi na shekara guda.

Alkali mai shari’a, Dimas Elishama ya samu ‘dan adawar da laifin amfani da kalaman batanci a kan shugabanni, tare da yunkurin jawo tashin-tashina a gari.

Dimas Elishama ya zartar da hukuncin shekara daya a gidan kaso a kan kowane laifin da ya aikata. Linda Ikeji ta ce hukuncin za su yi aiki ne a lokaci daya.

Buhari da Boss Mustapha
Shugaban kasa da Sakataren Gwamnatin Tarayya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mista Ikamu Hamidu Kato ya bayyana Muhammadu Buhari da Boss Mustapha da ‘mutane marasa amfani’, sannan ya kira SGF ‘shege da kare’ a wani bidiyo.

Yadda shari’ar ta kasance

Jami’an DSS sun fara gabatar da wanda ake zargi a kotu ta hannun ma’aikatar shari’a a makon da ya wuce, aka dakatar da shari’ar zuwa jiya, inda aka yanke hukunci.

Lauyoyin gwamnati sun gabatar da Zayyanu Adamu da Husseini Nakura a matsayin shaidu a kotu. An nuna faifen wannan mutum ya na zagin shugabannin kasar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Dage Sauraron Karar Hadiman Sunday Igboho, Ta Fadi Dalili

Kato ya amsa laifinsa, ya roki kotu ta yi masa rai, Alkali ya karbi korafinsa, ya amince da hakurin da ya bada, amma ya ce dole ne ya zama abin darasi domin 'yan gaba.

Ikama Hamidu Kato ya dauko fadan da ya karfinsa

A kwanaki baya kun ji cewa zagin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sakataren gwamnatin tarayya sun jawo an tsare Ikama Hamidu Kato a gidan kurkuku.

Baya ga haka, jami’yyar PDP ta dakatar da wannan Bawan Allah daga kujerar da yake kai na shugaban matasan na PDP a karamar hukumar Hong, Adamawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel