Ma'aikatan banki sun hadu da fushin doka bayan sun sace kudin mamaci a bankinsu

Ma'aikatan banki sun hadu da fushin doka bayan sun sace kudin mamaci a bankinsu

  • Hukumar EFCC ta yi nasarar daure wasu ma'aikatan banki da suka cinye kudin mamaci a bankinsu
  • Wannan ya faru ne a jihar Cross River a gaban wani alkalin kotu na jihar a jiya Laraba 4 ga watan Agusta
  • An yanke musu hukuncin da ya dace dasu, sannan an basu damar biyan beli idan suna da hali

Cross River - Hukumar EFCC, na yankin Uyo, ta tabbatar da hukunta wasu jami'an bankin guda biyu, Daniel Akpan Eno da Mbuk Idongesit, a gaban mai shari'a Edem Ita Kufre na babbar kotun jihar Cross River, Calabar saboda hadin baki da satar kudi a asusun wani abokin cinikinsu da ya mutu.

An yanke wa mutanen biyun hukuncin ne a ranar Laraba 4 ga Agusta, 2021 bayan sun amsa laifin da ke da alaka da hadin baki na aikata laifi da zamba, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wanda ake tuhuma na uku, kuma wanda ake zargi da hannu a barnar, Victor John Okon ba a kama shi da laifi ba. An daga shari’arsa zuwa ranar 10 ga watan Agusta, 2021 domin duba bukatar ba da belinsa.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS ta karyata zarginta da ake na tsare mutane ba bisa ka'ida ba

Ma'aikatan banki sun hadu da fushin doka bayan sun sace kudin mamaci a bankinsu
Jami'an EFCC | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Mai shari’a Kufre ya yanke hukunci ga Mista Akpan hukuncin daurin watanni ku tare da zabin biyan tarar Naira dubu hamsin (N50,000.00), yayin da aka yanke wa Mista Idongesit hukuncin daurin watanni uku tare da zabin biyan tarar Naira dubu talatin (N30,000.00).

Hukumar 'yan sanda ta bayyana irin matakin da za ta iya dauka kan Abba Kyari

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta bayyana cewa kora kai tsaye na daya daga cikin hukuncin da ka iya hawa kan mataimakin kwamishinan 'yan sanda (DCP), Abba Kyari, idan aka same shi da laifin da ake tuhumarsa da shi.

Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta dakatar da Kyari kwanan nan bayan da Amurka ta gabatar da zarginsa da hannu a zambar dala miliyan 1.1 da Ramon Abass, wanda aka fi sani da Hushipuppi ya aikata.

A bangaren Kyari, ya karyata dukkan wasu tuhume-tuhumen da ake akansa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta hana gwamnatin Buhari kame Sunday Igboho

Ofishin Abubakar Malami ya magantu kan zargin da ake wa Abba Kyari

A wani labarin, Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, kuma ministan Shari'a Abubakar Malami, ta ce har yanzu ba ta karbi wata takarda a hukumance daga cibiyar binciken Amurka ta FBI ba da ke neman damar kame mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari.

Wannan ya fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga ministan, Umar Gwandu yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar Punch.

FBI ta zargi Abba Kyari da karbar cin hanci daga hannun Hushpuppi, wani dan damfara dake fuskantar zaman kotu a Amurka, bayan kame masa wani abokin harkallarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel