Da duminsa: Cike da tashin hankali, Secondus ya koka kan yunkurin 'kwace' PDP

Da duminsa: Cike da tashin hankali, Secondus ya koka kan yunkurin 'kwace' PDP

  • Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, ya zargi wasu 'yan siyasa da yunkurin kwace jam'iyyar adawan
  • Secondus ya nuna damuwarsa da tashin hankalinsa inda ya zargi wasu 'yan siyasa da siyan 'yan jam'iyyarsa da kudi
  • Kamar yadda ya bayyana, ana kokarin tabarbara jam'iyyar PDP ne domin a kunyata shi tare da tozarta shi

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, ya koka cike da tashin hankali kan yadda ake yunkurin kwace jam'iyyar a Najeriya.

Babbar jam'iyyar adawan a cikin kwanakin nan tana fuskanta rikicin da bata taba gani ba a tarihinta, Daily Trust ta ruwaito.

Da duminsa: Cike da tashin hankali, Secondus ya koka kan yunkurin 'kwace' PDP
Da duminsa: Cike da tashin hankali, Secondus ya koka kan yunkurin 'kwace' PDP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito yadda bakwai daga cikin jami'an jam'iyyar na kasa suka yi murabus.

Sanata Joy Emordi ya koma APC

Washegarin da suka aje aiki, Sanata Joy Emordi, daya daga cikin 'yan kwamitin amintattu na jam'iyyar ya sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: PDP ta saki bidiyo, ta yanke muhimmiyar shawara

A wata takarda da Ike Abonyi, mai magana da yawunsa ya fitar a madadinsa, Secondus yace ana dab da kwace musu tsarin jam'iyya.

Secondus na zargin ana janye 'yan PDP da kudi

Ofishin yada labarai na shugaban jam'iyya na kasa na sane da kokarin da ake na lalata tsarin jam'iyyar wanda makasudin hakan shine bata sunan Uche Secondus, shugaban jam'iyyar na kasa.
Rahotannin da suka same mu sun bayyana cewa ana amfani da hanyoyi munana domin bata sunan shugaban jam'iyyar na kasa kuma ana son lalata tsarin jam'iyya.
A don haka muke sanar da jama'a ballantana gidajen yada labarai da masu ruwa da tsaki da su bude ido wurin kallo tare da gane duk wani ihisani da duk mai sharri zai yi wa dan jam'iyyarmu domin janye shi.
Abinda ya cigaba da baiwa 'yan jam'iyyar nan mamaki shine son sanin dalilin da yasa wannan mutumin ke ta kokarin janye jama'a da kudin gwamnati wanda aka ware domin cimma burika marasa kyau.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Manyan Shugabannin PDP Na Kasa 7 Sun Yi Murabus

Ana sauran watanni kalilan da muyi taron kasa, ya dace a ce duk mai yi wa jam'iyyarmu fatan alheri kuma yake kaunarta da ya bi koma yadda ya dace.
Uche Secondus ta kafar yada labarai yana son tabbatarwa masu ruwa da tsakin jam'iyyarmu cewa ana yin duk kokarin da ya dace wurin tabbatar da darajar jam'iyya ta dawo ba tare da wani bata lokaci ba ko nuna kosawa.

Fitacciyar jigon jam'iyyar APC ta sauya sheka, ta koma PDP

Mimi Adzape-Orubibi, tsohuwar 'yar takarar kujerar Sanata karkashin inuwar jam'iyyar APC a jihar Benue, ta mika wasikar barin jam'iyyar mai mulki.

A ranar Talata, 3 ga watan Augusta, Adzape-Orubibi ta sanar da The Sun cewa ta tura sanarwa a rubuce ga shugaban jam'iyyar na gundumar Kumakwagh dake karamar hukumar Kwande ta jihar, Honarabul Terwase Aheeve.

Kamar yadda jigon jam'iyyar APC tace, ta yanke wannan hukuncin ne bayan ta gane cewa jam'iyyar mai mulkin ba zata bata damar cikar burinta ba.

Kara karanta wannan

Manyan jami’an jam’iyyar PDP na kasa 7 sun yi murabus daga mukamansu

Asali: Legit.ng

Online view pixel