Karin Bayani: Jiga-Jigan PDP Sun Shiga Taron Gaggawa Kan Wani Sabon Rikici da Ya Kunno

Karin Bayani: Jiga-Jigan PDP Sun Shiga Taron Gaggawa Kan Wani Sabon Rikici da Ya Kunno

  • Sabon rikici ya barke a shugabancin jam'iyyar PDP ta kasa inda wasu mutum 7 suka yi murabus
  • Mambobin kwamitin gudanarwa bakwai da suka yi murabus sun zargi shugabancin PDP da son rai
  • A halin yanzu shugabannin PDP na kasa sun shiga taron gaggawa a Abuja domin tattaunawa kan lamarin

FCT Abuja:- Shugabannin babbar jam'iyyar hamayya PDP sun shiga taron gaggawa bayan manyan jiga-jiganta 7 sun mika takardar murabus, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Manyan yan kwamitin gudanarwa bakwai a wasiku daban-daban da suka aike wa sakataren jam'iyyar PDP na kasa ranar Talata, sun yi zargin rashi adalci da kuma watsar da su da shugaban PDP na kasa, Uche Secondus ya yi.

Wata majiya ta bayyana cewa wannan murabus ɗin na ɗaya daga cikin rikicin da ya taso a jam'iyyar PDP domin canza shugabancinta.

Shugaban PDP na kasa, Uche Secondus
Yanzu-Yanzu: Jiga-Jigan PDP Sun Shiga Taron Sirri Na Gaggawa Kan Wata Babbar Matsala da Ta Taso Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Mambobin kwamitin gudanarwa 7 sun yi murabus

Wasu mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyyar PDP ta kasa sun yi murabus domin nuna rashin jin daɗinsu da yanayin shugabancin.

The Cable ta rawaito cewa mutanen da suka yi murabus sun hada da mataimakin sakataren kudi, mataimaki kan harkokin shari'a,

Sauran sun haɗa da akawu mai bincike kan harkokin jam'iyya, mataimakin sakataren yaɗa labarai, shugabar mata da mataimakin sakataren shirye-shirye.

Waɗanda suka yi murabus ɗin sun zargi cewa akwai rashin tsari na shugabanci da san rai a harkokin shugabancin jam'iyyar.

A wani labarin kuma Hotunan Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu da Wani Gwamna a Birnin Landan

Yayin da ake zargin jagoran jam'iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu na jinya ne a birnin Landan.

Wasu magoya bayansa sun bayyana hotunansa tare da gwamnan Lagos, Babajide Sanwo Olu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel