Daya daga cikin 'yammatan Chibok da mijinta dan Boko Haram sun mika wuya ga sojoji

Daya daga cikin 'yammatan Chibok da mijinta dan Boko Haram sun mika wuya ga sojoji

  • Tsohuwar dalibar GSS Chibok dake jihar Borno, da mijinta, dan Boko Haram, sun mika wuyansu ga sojojin Najeriya
  • Dalibar tana daya daga cikin daliban makarantar guda 200 da ‘yan Boko Haram suka sata a ranar 14 ga watan Afirilun 2014
  • Duk da dai ana zargin duk da barkewar cuta, bakar yunwa da kuma bamabaman da sojojin sama dana kasa suke auna musu

Maiduguri, Borno - Tsohuwar dalibar GSS Chibok dake jihar Borno da mijinta, dan Boko Haram sun mika wuyansu ga sojojin Najeriya kamar yadda PRNigeria ta tabbatar.

Dalibar tana daya daga cikin dalibai 200 da ‘yan Boko Haram aka sata a ranar 14 ga watan Afirilun 2014.

Daya daga cikin 'yammatan Chibok da mijinta dan Boko Haram sun mika wuya ga sojoji
Daya daga cikin 'yammatan Chibok da mijinta dan Boko Haram sun mika wuya ga sojoji. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sojoji basu sanar da sunan dalibar ba

Duk da dai sojojin basu sanar da sunan dalibar ba, amma an tabbatar da yadda ita da mijinta suka sanar da tubansu daga kungiyar.

An tattaro bayanai akan yadda suka mika wuya kuma suka zubar da makamansu ga dakarun sojin a wani wuri dake kusa da tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Bidiyon sojojin Najeriya suna raka yara makaranta a yankin arewa maso gabas

Akwai wasu 'yan ta'addan Boko Haram dake son mika wuya

Wani jami’in binciken sirri ya sanar da PRNigeria cewa akwai wasu ‘yan boko Haram da suka samu sojoji suna nuna yadda suke son su tuba su zubar da makamansu.

Yan ta’addan suna shirin mika wuya kuma kila hakan yana da alaka da lalata sansaninsu da sojojin sama suke yi da kuma ragargazarsu da sojin kasa suke yi da kuma barkewa cutuka tare da bakar yunwa da suka riski ‘yan ta’addan.
Akwai ‘yan boko Haram da dama da kwanannan zasu bayyana kawunansu don su tuba amma ba lallai sojoji su yarda ba saboda tsaron kasa,”a cewar jami’in.

Jiragen NAF sun ragargaji motocin yakin Boko Haram, sojin kasa sun sheke 'yan ta'adda

Hadakar rundunonin sojin kasa da na sama sun ragargaji ‘yan ta’addan Boko Haram-ISWAP a wuraren Gubio dake jihar Borno.

Wani jami’in binciken sirri ya sanar da PRNigeria cewa a kalla motocin yaki hudu sojojin sama dana kasa suka lalata yayin ragargazar ‘yan ta’addan.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sojoji sun ceto daliban da aka sace a Kaduna daga 'yan bindiga

Lamarin daya faru ne a ranar Litinin ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan ta’addan da dama. PRNigeria ta fahimci yadda rundunar sojin kasa suka fuskanci ‘yan ta’addan yayin da jirgin sojojin NAF kuma ya fita wani aikin na daban aka umarce shi da ya cigaba da aiki a wuraren Gubio.

Asali: Legit.ng

Online view pixel