Kasar Amurka ta yi wa Gwamnatin Buhari kaca-kaca a kan haramta aiki da Twitter

Kasar Amurka ta yi wa Gwamnatin Buhari kaca-kaca a kan haramta aiki da Twitter

  • Kasar Amurka ta tanka Najeriya kan matakin dakatar da amfani da Twitter
  • Gwamnatin Joe Biden ta ce bai dace a haramta Twitter a damukaradiyya ba
  • Sakataren gwamnatin Amurka ya yi kira ga Kasar ta janye wannan mataki

Ofishin sakataren gwamnatin kasar Amurka ta yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya ta janye matakin da ta dauka na dakatar da kamfanin Twittter.

Jaridar The Cable ta ce kasar Amurka ta fitar da sanarwa a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, 2021, inda ta nuna rashin goyon bayan matakin da aka dauka.

Gwamnatin Joe Biden ta bakin Anthony Blinket, ta ce tana goyon bayan duk wani yunkuri da Najeriya ta ke yi na ganin kawo zaman lafiya da hadin-kai.

KU KARANTA: Lauyoyi za su yi shari'a da Gwamnati saboda hana Twitter

Sai dai Amurkar ta ce dole ne Muhammadu Buhari ya girmama ‘yancin ‘yan kasarsa. Daily Trust ta rahoto kasar tana cewa kowa ya na da damar yin magana.

Kamar yadda jaridar The Nation ta fitar da rahoto a jiya, jawabin da Mai magana da yawun bakin ofishin sakataren gwamnatin Amurka, Misa Ned Price ya ce:

Amurka ta soki dakatarwar da gwamnatin Najeriya ta yi wa Twitter, sannan ta ke barazanar kama duk ‘Dan Najeriyar da ya yi amfani da Twitter, ta kai shi kotu.”

“Hana mutanen Najeriya dauka, tattara, da yada rahotanni da ra’ayoyi da bayanai ba ya cikin tsarin damukaradiyya.” Inji Ned Price a madadin Anthony Blinken.

KU KARANTA: Rauf Aregbesola ya yi kira ga jama’a su guji kiran a barka Najeriya

Sakataren gwamnatin Amurka
Sakataren gwamnatin Amurka, Anthony J. Blinken Hoto: www.timesofisrael.com
Asali: UGC

Ya ce: “’Yancin yin magana da neman bayanai ta kafar yanar gizo da wajen shafin intanet sune tubulin da suka kafa tsarin damukaradiyya da zai kawo cigaba.”

“Muna goyon bayan Najeriya yayin da ta ke neman kawo hadi-kai, zaman lafiya da cigaba.

A matsayinmu na abokiyar aikinta, muna yin kira ga gwamnati ta girmama damar ‘yan kasarta na fadin abin da suka ga dama, ta hanyar janye dakatarwar.” inji sa.

A ranar Alhamis aka ji cewa Alkali ya yanke hukuncin daurin watanni hudu ga mutumin da ya mari Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron a bainar jama’a.

Watakila Matashin da ya mari Emmanuel Macron ba zai je kurkuku ba. Damien Tarel ya ce abubuwa su na sukurkucewa ne, don haka ya mari Shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel