Buhari a Landan: Burtaniya ta shirya taimakawa Najeriya a yaki da matsalar rashin tsaro

Buhari a Landan: Burtaniya ta shirya taimakawa Najeriya a yaki da matsalar rashin tsaro

  • Kasar Burtaniya ta amince da taimakawa Najeriya wajen yakar ta'addancin da Najeriya ke yi
  • Firaministan Burtaniya ne ya bayyana haka yayin da ya gana da shugaban kasar Najeriya, Buhari
  • Wannan na zuwa ne yayin da shugaba Buhari ya halarci taron habaka a babban birnin Landan

Firaministan Burtaniya, Boris Johnson, ya ce kasarsa a shirye take domin taimakawa Najeriya wajen yaki da matsalolin rashin tsaro da suka addabi kasar, BBC ta ruwaito.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya fitar, Boris Johnson ya ba shugaba Buhari tabbacin goyon bayan ne lokacin da ya gana da shugaba Buhari a gefen taron da ke gudana na habaka ilimi a Landan.

Shugabannin biyu sun kuma daddale cewa ya kamata a ba tsarin shari’a damar gudanar da ayyukanta bayan tantance yakin da ake yi da nau’ikan ta’addanci daban-daban a Najeriya.

Buhari a Landan: Burtaniya ta shirya taimakawa Najeriya a yaki da matsalar rashin tsaro
Shugaba Buhari da Boris Johnson | Hoto: dailypost.ng
Asali: Twitter

Shugabannin biyu sun ce yana da mahimmanci tsarin shari'ar ya gudana ba tare da tsangwama ba, ko ma wanene ke fuskantarta.

Kara karanta wannan

Minista Lai Mohammed ya magantu kan matsalolin kabilanci da addini a Najeriya

Sauran batutuwan da shugabannin suka tattauna akai

Buhari ya yi wa Firaministan bayani game da bukatar wutar lantarki da kokarin da ake yi a Najeriya, da kuma shirye-shiryen da aka tsara domin cimma nasarar wadatar abinci, Daily Trust ta tattaro.

Sanarwar ta kara da cewa, shugabannin biyu, sun tattauna kan yadda za a bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen biyu, bunkasa hasken rana da iska, jagorancin kungiyar kasashe gama gari da zai ci gaba da sauran batutuwan da suka shafi kasashen biyu.

PDP ta caccaki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan, ta ce ya yaudari 'yan Najeriya

A wani labarin, jam'iyyar PDP ta soki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan domin duba lafiya da kuma halartar wani taron koli kan fannin ilimi duk dai a Landan din, jaridar Punch ta ruwaito.

PDP ta ce, tafiyar shugaban ba komai bane face son amfani da albarkatun kasa don halartar taro wanda zai iya halartar ta yanar gizo; kamar yadda wadanda suka shirya taron suka tsara.

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

PDP ta kuma yi Allah wadai da Fadar Shugaban Kasa kan kokarin boye ganawarsa ta sirri da likitocinsa a karkashin taron da zai halarta, tare da yin tir da rashin cika alkawuran shugaba Buhari na zaben 2015 cewa ba zai je kasar waje domin duba likita ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel