Rikicin APC: Yadda Gwamna Buni da Minista su ka sabawa umarnin Mataimakin Shugaban kasa

Rikicin APC: Yadda Gwamna Buni da Minista su ka sabawa umarnin Mataimakin Shugaban kasa

  • An soma zaben shugabannin APC duk da wani hukunci da kotun koli ta zartar
  • Mataimakin Shugaban kasa ya bada shawarar APC ta dakata da batun yin zabe
  • Mala Buni da Abubakar Malami sun ki yin na’am da shawarar Yemi Osinbajo

Abuja - Ganin halin da APC ta shiga, tare da cewa ba ya kasar, shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Yemi Osinbajo ya jagoranci ragamar jam’iyya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Yemi Osinbajo a makofinsa

Jaridar This Day ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba matakinsa dama ya dauki matakin da zai ceci jam’iyyar APC a gaban kotu.

Shugaban kasa ya na Landan, don haka ya nemi Farfesa Yemi Osinbajo ya wakilce sa wajen daukar mataki.

Rahoton ya bayyana cewa ba tare da wani bata lokaci ba, mataimakin shugaban Najeriyar ya tara duk lauyoyin da suke gwamnati domin ya dauki matsaya.

An tsara APC za ta shirya zabukan mazabu ne a ranar Asabar, 31 ga watan Yuli, 2021, don haka Osinbajo ya nemi ayi maza a san matakin da za a dauka.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Dage Sauraron Karar Hadiman Sunday Igboho, Ta Fadi Dalili

Yadda taron ya kasance

A wajen wannan taro, baki ya hadu a kan cewa a dakatar da maganar shirya zabuka a lokacin. Abubakar Malami SAN ne kadai ya saba wa wannan ra’ayi.

Wadanda suka halarci wannan zama sun hada da Ministoci irinsu Babatunde Fashola SAN, Lai Mohammed, Festus Keyamo da kuma Farfesa Tahir Mamman.

Yemi Osinbajo a taron FEC
Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo a Aso Villa Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Farfesa Tahir Mamman masanin shari'a ne, kuma ya na cikin kwamitin shirya zabukan APC.

A nan aka yi ta tafka muhawara, aka kawo shawarar APC ta ajiye batun gudanar da zabukan shugabanninta, amma a karshe sai akasin hakan ne ya faru.

Ministan shari’a na kasa, Abubbakar Malami bai yarda da duk abubuwan da aka fada ba, ya ce za a iya gudanar da zabukan kamar yadda aka tsara tun farko.

Ganin haka ne Farfesa Osinbajo ya yi yunkurin tuntubar mai girma shugaban kasa a waya, amma bai same shi ba, daga nan sai ya nemi gwamna Mai Mala Buni.

Kara karanta wannan

Hushpuppi: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya gaya wa Buhari abin da ya kamata ya yi na mika Abba Kyari

Jaridar ta ce nan take shugaban rikon kwaryan na APC, Mala Buni ya nuna wa Osinbajo sai an yi wannan zabe, ya karkata da ra'ayin lauyan gwamnatin tarayya.

A wani rahoto, Daily Trust ta ce gwamna Buni da Ministan shari'ar sun musanya wannan zargi, sun ce ba a saba wa Osinbajo ba, asali ma bai bada wani umarni ba.

Hukuncin kotun koli ya jawo wa APC shakku

A baya an ji Festus Keyamo ya rubuta wa shugabannin jam’iyyar APC wata wasika a boye. Ministan ya bada shawarar janye maganar zaben shugabanni.

Keyamo ya ce hukuncin Alkalan kotun koli a kan zaben gwamnan jihar Ondo ya nuna tun farko bai dace Mala Buni ya hau kujerar shugaban jam'iyyar APC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng