Karin Bayani: Fusatattun Daliban Wata Jami'an Sun Toshe Babbar Hanya Saboda Sheke Dan Uwansu

Karin Bayani: Fusatattun Daliban Wata Jami'an Sun Toshe Babbar Hanya Saboda Sheke Dan Uwansu

  • Wasu fusatattun ɗaliban jami'ar FUTA sun toshe babbar hanyar Akure-Ilesa
  • Daliban sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne domin nuna bacin ransu kan abinda masu gadin jami'a suka musu
  • Zanga-zangar dai ta tara dandazon mutane matafiya yayin da ɗaliban suka hana su wuce wa

Akure, Ondo:- Wasu fusatattun ɗalibai na jami'ar fasaha ta tarayya dake Akure (FUTA), jihar Ondo, sun toshe babbar hanyar Akure-Ilesa, kamar yadda punch ta ruwaito.

Rahoto ya nuna cewa ɗaliban sun ɗauki wannan matakin ne domin zanga-zangar kashe ɗan uwansu ɗalibi, wanda ya mutu a sanadin hatsari ranar Litinin da yamma.

Masu zanga-zangan sun bayyana cewa jami'an tsaron jami'ar FUTA sun ki buɗe musu kofa domin sukai ɗalibin asibiti bayan hatsarin.

Daliban FUTA sun fito zanga-zanga
Da Duminsa: Fusatattun Daliban Wata Jami'an Sun Toshe Babbar Hanya Saboda Sheke Dan Uwansu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ɗaliban sun bayyana cewa wanda hatsarin ya rutsa da shi ka iya rayuwa inda an kai shi asibiti cikin lokaci.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa zanga-zangar ɗaliban ta jawo taruwar dandazon matafiya a kan hanyar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyukan Kaduna, Sun Hallaka Aƙalla Mutum 18

Mai magana da yawun jami'ar FUTA, Mr Adengbenro Adebanjo, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Gwamnati ta fi gane yaren yajin aiki

Shugaban ƙungiyar likitoci ta ƙasa (NARD), Dakta Akanimo Ebong, yace FG bata nemansu a tattauna har sai sun tsunduma yajin aiki.

Shugaban yayi wannan jawabi ne yayin da yake zantawa da kafar watsa labarai ta Channels tv a shirinta na 'Sunrise Daily' ranar Litinin.

Ƙungiyar NARD ta sanar da fara yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Litinin 2 ga watan Agusta saboda gazawar gwamnati na biyansu albashi da kuma wasu alawus.

A wani labarin kuma Yan Fansho Sun Aike da Wata Muhimmiyar Wasika Ga Shugaba Buhari

Wasikar yan fanshon dai godiya ce da fatan alkairi biyo bayan biyansu wasu kuɗaɗe da suke bin gwamnatin tarayya bashi da shugaban yayi.

Takardar wasikar wacce take ɗauke da sanya hannun shugaban yan fansho na kasa, Elder Actor Zal, da kuma sakatarensa, sun jinjina wa shugaba Buhari bisa wanna namijin kokari.

Kara karanta wannan

Zamu Tona Asirin Yan Ta'addan Cikin Mu, Shugabannin Fulani Sun Yi Alkawari

Asali: Legit.ng

Online view pixel