Bidiyon wani rigimammen mutum da ya makale a gaban adaidaita sahu da ke tafiya saboda direban ya ki basa kudi

Bidiyon wani rigimammen mutum da ya makale a gaban adaidaita sahu da ke tafiya saboda direban ya ki basa kudi

  • Wani rigimammen dattijo ya sanya kansa a hadari don samun kudi daga direban adaidaita sahu yayin da ya makale a gaban keken da ke tafiya
  • Kan haka har sai da wata iska mai karfi ta cire masa hula, sai dai hakan bai sa ya saduda ba, ya jajirce ga karbar N50 daga direban
  • 'Yan Najeriya da suka mayar da martani kan bidiyon sun ce abun da mutumin ya aikata ya nuna lallai talauci babban cuta ne

Wani da ake zargin jami'in doka ne ya haifar da ‘yar dirama a yayin da yake kokarin samun kudi daga direban adaidaita sahu lamarin da ya haifar da cece kuce a cikin mutane.

A cikin wani ɗan gajeren bidiyon da @Instablog9ja ya wallafa, an gano mutumin makale a gaban adaidaita sahu, yana fuskantar direban sosai.

Bidiyon wani rigimammen mutum da ya makale a gaban adaidaita sahu da ke tafiya saboda direban ya ki basa kudi
Duk da hularsa ta cire, mutumin bai saduda ba Hoto: @Instablog9j
Asali: Instagram

Ya jajirce da son karbar kudi daga hannun direban

Jami'in bai yi kasa a gwiwa ba yayin da adaidaita sahun ya ci gaba da tafiya cikin gudu. An rahoto cewa yana kokarin karbar N50 daga hannun direban ne.

Kara karanta wannan

Allah Zai Wanke Abba Kyari, Hassada Wasu Ƴan Sanda Ke Masa: Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin ‘Brekete Family’

An jiyo fasinjojin adaidaitan suna gargadinsa kan abun da yake aikatawa wanda yake ba daidai ba kuma mai cike da hatsari.

Kalli bidiyon a kasa:

Ya saka rayuwarsa cikin hatsari

A lokacin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya tattara sharhi sama da 6,000 tare da dubban mutane da suka kalli bidiyon.

Legit.ng ta tattara wasu daga cikin martanin a ƙasa:

futballpunter ya ce:

“Daga lokacin da hular ta tashi daga kan baba, ya kamata ya san cewa ya kwabsa.”

sixtrading ya ce:

"Lokacin da hularsa ta fita ya san cewa hukuncin da ya yanke ba daidai bane."

mrs_aproko9ja1 ta ce:

"Kana wasa da mutumin da ke da kwalin hoton naira marley?"

malikdeking ya ce:

"Kana jefa rayuwar ka cikin hadari saboda Naira 50, dole sai an yaki talauci."

Abun mamaki: Hotunan yarinya ƴar firamare tana gyaran motoci ya jawo cece kuce a yanar Gizo

Kara karanta wannan

Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano

A wani labarin, wata yarinya 'yar makarantar firamare ta haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan hotunanta sun bayyana inda take gyaran motoci.

Da ya wallafa labarin a shafin Twitter tare da hotunan ta a bakin aiki, @AD_Kwatu ya ce yarinyar da aka bayyana da suna Khadija ta kasance mai gyaran motoci wacce ta kware wajen gyaran birki kuma har yanzu tana zuwa makaranta duk da aikin ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel