Allah Zai Wanke Abba Kyari, Hassada Wasu Ƴan Sanda Ke Masa: Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin ‘Brekete Family’

Allah Zai Wanke Abba Kyari, Hassada Wasu Ƴan Sanda Ke Masa: Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin ‘Brekete Family’

  • Ahmed Isah, mai watsa labarai da ke gabatar da shirin Brekete Family ya yi magana game da dambarwar da Abba Kyari ya shiga
  • Isah ya bayyana cewa yana tare da Abba Kyari kuma yana fatan Allah zai wanke shi daga wannan zargin da ake masa
  • Dan jaridar da ake yi wa lakabi da Ordinary President ya kara da cewa ko zargin gaskiya ne ba abinda zai sami Kyari saboda alherinsa ya fi kuskuren

Ahmad Isah, mai watsa labarai kuma wanda ya kafa gidan rediyo na kare hakkin biladama, Brekete Family, ya ce Abba Kyari, mataimakin kwamishinan yan sanda ya aikata alheri sosai don haka kuskure ba za ta yi sanadin rushewarsa ba, rahoton Daily Trust.

A halin yanzu rundunar yan sandan Nigeria ta dakatar da Kyari sakamakon tuhumarsa da laifi da FBI na Amurka ke yi.

Allah Zai Wanke Abba Kyari, Hassada Wasu Ƴan Sanda Ke Masa: Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin ‘Brekete Family’
DCP Abba Kyari da aka dakatar bisa zarginsa da karbar cin hanci daga hannun Hushpuppi. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ramon Abbas, biloniya da ake zargi dan zamba ne, da aka fi sani da Hushpuppi, ya yi ikirarin cewa ya bawa Kyari cin hanci domin ya kama wani da ya masa dabara yayin zambar $1.1m.

Kara karanta wannan

Sabon Bincike: Yadda Hushpuppi ya aika wa Abba Kyari miliyoyi na wata harkalla

Isah, yayin da ya ke magana da shirin safe a gidan rediyon 101.1 FM Abuja a ranar Talata, ya ce ba daidai bane Amurka ta bukaci a mika mata Kyari.

Ya ce:

"Wannan abin da Abba Kyari ya shiga, yan sanda da dama suna murna, yan sanda wadanda ba su san makamashin aiki ba. Wasunsu babu abin da suka iya sai gulma, wasun su da suke mata, maza ne, amma mata ne ga shugabanninsu."
"Suna murna, sunyi gaggawan murna amma bari in fada maka, ko da ba ka son saurara, da izinin Allah babu abin da zai samu Abba Kyari. Ya yi aikin alheri sosai da za a rushe shi saboda laifi daya, ko da ma gaskiya ne.
"Amurka ba za ta fada mana yadda za mu yi rayuwarmu ba, Amurka ba aljanna bane. Akwai mutane da ba su da gidaje a Amurka, akwai marasa aikin yi, akwai masu shan wiwi, akwai masu shan koken, akwai makasa, don haka mene za su fada mana, shin Amurka ta fi Afirka ne idan ba don rashin shugabanci mai kyau ba?

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Abba Kyari, Singham ya yi zazzafan martani kan 'yan sanda

"Mene suke da shi da bamu da shi? Muna tare da Abba Kyari, kuma Allah zai wanke shi.
"Wata rana, wannan mutumin zai zama IGP, suna masa hassada ne saboda kwarewarsa wurin aiki, ba za su iya rabin abin da ya ke yi ba. Ya fi su fasaha da basira sosai. Shi mutum ne mai kankan da kai, baya da girman kai."

'Yan Sanda Sun Kama Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin 'Brekete Family'

A baya, mun kawo muku cewa 'Yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.

Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".

Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.

Kara karanta wannan

Gaskiya: Yadda matashi ya mayar da 2500000 da aka tura asusun bankinsa cikin kuskure

Asali: Legit.ng

Online view pixel