Gwamnonin PDP sun magantu bayan ficewar wasu manyan jam'iyyar jiya Talata
- Kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP sun magantu bayan ficewar wasu manya a jam'iyyar
- Gwamnonin sun ce, duk wani dan jam'iyyar da ke jinta a ransa ya kwantar da hankalinsa
- A cewar gwamnonin, wannan ba komai bane, kuma suna aiki don dinke wannan barakar
Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta yi kira ga mambobi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da su kwantar da hankulansu kan murabus din wasu mataimaka na jam’iyya bakwai a ranar Talata.
Kungiyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da shugabanta kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya fitar a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.
Mista Tambuwal ya bukaci duk mambobin jam'iyyar da abin ya shafa da su yi wa jam'iyyar fatan zaman lafiya, domin kuwa mambobin na ci gaba da kokarin shiga cikin lamarin.

Asali: UGC
Ya bayyana cewa kungiyar ta yi nadama da bakin ciki na rigingimun da suka faru kwanan nan a PDP.
A cewarsa:
“Don haka gwamnonin ke kira ga dukkan membobin jam’iyyar da kuma duk masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankulansu yayin fuskantar lamarin.
"Muna rokon duk wadanda abin ya shafa da wadanda ke da muradin jam'iyyar PDP a zuciya da su mai da wukar da suka zare.
"Ana kokarin shawarwari tare da membobin kwamitin amintattu na jam'iyyar ta PDP da sauran masu ruwa da tsaki don warware dukkan batutuwan da ke gaba."
PDP ba sa'ar APC bace: PDP ta yi martani kan Jega bisa kwatanta ta da APC
Jam'iyyar PDP ta ce, ba daidai bane wani ya tsaya yana kwatanta nasarorinta da na jam'iyyar APC mai mulki a yanzu ba, jaridar Sun ta ruwaito.
Wannan na fito wa ne daga bakin kakakin ta na kasa, Kola Ologbondiyan a jiya Litinin 2 ga watan Agusta yayin da ya yake martani ga kalaman tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.
Legit.ng ta tattaro cewa Ologbondiyan ya ce yayin da PDP a cikin shekaru 16 na mulkinta ta biya bashin kasar tare da sake farfado da tattalin arziki gami da manyan ayyuka da aka samar ga 'yan kasa, APC ta lalata tattalin arzikin kasar ne.
Duk lalacewa mun fi PDP: APC ta caccaki Attahiru Jega bisa kwatanta ta da PDP
A wani labarin daban, jam'iyyar APC ta mayar da martani kan maganganun baya-bayan nan da aka danganta ga tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega.
Jega ya shawarci ‘yan Najeriya da kada su zabi jam’iyya mai mulki APC da jam’iyyar adawa ta PDP a babban zaben 2023.
Wata sanarwa da mukaddashin sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata John James Akpanudoedehe ya aikewa Legit.ng a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki bata ji dadin kwatanta ta da PDP ba.
Sashin sanarwar ya ce:
“An jawo hankalin mu ga rashin kulawa, ba daidai ba, da hargitsi na siyasa wanda tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega ya yi inda ya yi wa APC, tare da PDP kudin goro.
“Yayin da PDP ta kasa cimma burin 'yan Najeriya a matsayin gwamnati da kuma jam’iyyar adawa, APC na ci gaba, na cikin koshin lafiya kuma tana tsaftace babban barnar da PDP ta bari wanda ta kasa samar da romon dimokuradiyya ga al’ummar Najeriya bayan shekaru 16.
“Yayin da Farfesa Jega ya fadi gaskiya game da PDP, jam’iyyar da a karkashinta ya kasance shugaban hukumar gudanar da zabe ta kasa, mun ki amincewa da kwatanta APC da PDP.
Asali: Legit.ng