Tunji Disu: Abubuwa 8 da ya dace a sani game da magajin Abba Kyari a tawagar IRT

Tunji Disu: Abubuwa 8 da ya dace a sani game da magajin Abba Kyari a tawagar IRT

  • A farkon makon nan IGP Usman Alkali Baba ya nada sabon shugaban IRT
  • Tunji Disu aka zaba a madadin Abba Kyari da aka dakatar a ranar Lahadi
  • Hukumar FBI na zargin DCP Abba Kyari da hannu a badakalar Hushpuppi

Abuja - A ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, 2021, Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya ya nada Tunji Disu a matsayin sabon shugaban dakarun IRT.

Kamar yadda ‘yan sandan Najeriya suka bada sanarwa, IGP Usman Baba ya nada DCP Tunji Disu ne domin ya maye gurbin Abba Kyari da aka dakatar.

CP Frank Mba ya ce Usman Alkali Baba, psc (+), NPM, fdc ya amince da aika DCP Tunji Disu a matsayin sabon shugaban rundunar ‘yan sanda ta IRT.

Wanene DCP Tunji Disu?

1. Sabon shugaban tawagar IRT ya yi digirinsa a fannin harshen turanci a Jami’ar jihar Legas wanda aka fi sani da LASU.

2. Daga nan ya koma karatu, ya samu digiri na biyu a fannin ilmin gudanar da aiki a Jami’ar Adekunle Ajasin da ke Ondo.

Kara karanta wannan

Ayi hattara, sabon samufurin COVID-19 ya shiga Abuja, da wasu Jihohi 7 inji Gwamnatin Tarayya

3. Disu ya yi kwas na kware wa iri-iri a gida da kasashen waje. Daga ciki ya samu horo a Legas, Jos da kasashen Botswana da Ingila domin sanin makaman aiki.

4. DCP Disu ya na cikin kungiyoyi da suka hada da na shugabannin ‘yan sanda na kasa, kwararru a kan harkar wayar da kan al’umma da dai sauransu.

Abba Kyari da Tunji Disu
Abba Kyari da Tunji Disu Hoto: www.774ngr.com da www.dailypost.ng
Asali: UGC

Tunji Disu ya rike mukamai da dama a gidan soja, daga ciki:

1. Tunji Disu ya jagoranci tawagar kar-ta-kwana watau RRS na reshen jihar Legas.

2. Sanarwar ta ce Tunji Disu ya rike mataimakin kwamishina a hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja.

3. DCP Disu ya taba zama shugaban sashen CID masu binciken masu laifi na reshen jihar Ribas.

4. Disu ya rike jagoran tawagar ‘yan sandan Najeriya da aka tura zuwa Dafur, kasar Sudan domin su kawo zaman lafiya a karkashin shirin AU.

Abba Kyari ya bar ofis

Kafin yanzu DCP Abba Kyari ne ke rike da wannan runduna ta musamman da ke samun bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Kwamitin jami'an tsaro mai mutum 4 da zai binciki Abba Kyari ya fara aiki bayan dakatarwa

Idan za a iya tuna wa, rundunar 'yan sandan Najeriya ta dakatar da Abba Kyari daga aiki ne bayan FBI ta zarge shi da karɓar cin hanci a hannun 'dan 419.

Asali: Legit.ng

Online view pixel